TAZARAR HAIHUWA: Gwamnatin Najeriya ba ta ware wa shirin ko sisi ba a kasafin 2022

Hukumar kidaya ta ƙasa NPC ta bayyana cewa adadin yawan mutanen dake Najeriya ya kai miliyan 206 a shekaran 2020.

Hukumar ta yi hasashen cewa nan da shekaran 2050 Najeriya za ta zama ƙasa ta uku a jerin kasashen da suka fi yawan mutane a duniya ban da Chana da India.

Bincike ya nuna cewa yadda mutane ke karuwa ba haka bane tattalin arziki, ababen more rayuwa da samun aiki ke karuwa ba a kasan.
Wannan matsala da Najeriya ke fama da shi itace sillar bullowar matsalolin rashin tsaro, tallauci da sauran matsalolin da kasan ke fama da su.

Duk da haka a kasafin kudin shekarar 2022 gwamnati bata ware kudade ba domin samar da dabarun bada tazarar haihuwa ba.

Fannin kiwon lafiya ta samu kasa da kashi biyar a cikin kasafin kudin shekarar 2022 wanda hakan ya saba wa tsarin ware akalla kashi 15% na kasafin kudin shekara wa fannin kiwon lafiya da kasashen Afrika suka amince su yi a shekarar 2001 a Abuja.

A cikin kasafin kudin shekarar 2022 wanda shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisun kasa fannin lafiya ta samu kason Naira biliyan 816 da yayi daidai da kashi 4.93 cikin 100 na kasafin.

Kasafin kudin fannin kiwon lafiya

Gwamnati ta gabatar da Naira tiriyan 16.39 kasafin kudin shekarar 2022.

Gwamnati ta ware wa fannin lafiya Naira biliyan 816 daga cikin Naira tiriyan 16.39 inda a ciki fannin kiwon lafiya za ta yi amfani da kashi 57% wajen hidimominta na yau da kullun, kashi 24% don aiwatar da manyan ayyukan a ma’aikatar.

Daga cikin kudaden akwai kason tallafin Naira biliyan 104.87 daga kamfanin GAVI da naira biliyan 54 daga kason kashi daya ga gwamnati ta ware domin fannin lafiya na BHCPF.

A wani taro da aka yi a Abuja domin tattauna matsalar rashin ware wa bada tazarar haihuwa kudade kungiyar ‘Partnership for Advocacy on Child and Family Health (PACFaH@Scale)’ ta bayyana cewa ga dukan alamu gwamnati ba a shirye take ta Samar da dabarun bada tazaran haihuwa a kasar nan ba duk da yadda ake kara yawa a kasar.

Kungiyar ta ce rashin haka zai kawo koma baya a ci gaba da kasar da samu wajen bada tazarar iyali.