TASHIN HANKALIN ZAMFARA: ‘Yan bindiga sun sako ɗaliban Maradun 75 bayan kwana 12 da kwashe su

An tabbatar da kuɓutar ɗalibai 75 na Makarantar Sakandaren Je-ka-ka-dawo ta Ƙaya da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
An saki ɗaliban 75 bayan sun shafe kwanaki 12 a hannun ‘yan bindiga.
Makonni biyu ne wannan jarida ta buga labarin yadda aka sace ɗaliban a Maradun, mahaifar Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara.
Bayan san sako su dai an zarce tare da su da wani malamin su ɗaya zuwa Gidan Gwamnanti, inda Gwamna Matawalle ya gana da su.
“An tabbatar da cewa an sako ɗalibai 75 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su, makonni biyu da su ka gabata a Ƙaya, cikin Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.”
An sako ɗaliban a daidai lokacin da sojoji ke ɓarin-wuta a cikin dazukan Zamfara a kan ‘yan bindiga.
Cikin makonni biyu ne aka rufe kasuwanni da kuma hana zirga-zirgar kayan abinci da dabbobi a jihar.
An kuma hana saida fetur ga masu galan da jarka.
Bello Matawalle ya bayyana cewa ba zai yi sulhu da ‘yan bindiga ba.
Ya ce babu sauran sasantawa da ‘yan bindiga, tsakanin mu da su sai kisa kawai, inji Matawalle.
Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bayyana cewa daga yanzu Gwamnatin Jihar Zamfara ba za ta sake nema ko yarda ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba.
Ya ce saboda an sha yi masu wannan tayin a baya, kuma su na karya alƙawari da saɓa yarjejeniyar da aka yi da su.
Da ya ke magana a Gusau, Matawalle ya ce maimakon a yi sulhu da su, ya na kira ga jami’an tsaro su ci gaba da zaƙulo kamar ɓeraye a cikin daji, su na rafke su kawai.
“Gwamnati na ba za ta sake bai wa ‘yan bindiga afuwa ba, saboda an sha yi masu afuwa a baya, amma su na tayar da tubar su.”
Daga nan sai ya roƙi al’ummar jihar Jigawa su ƙara juriya da haƙuri tare da goyon bayan tsauraran matakan da jami’an tsaro ke ɗauka, su na zaƙulo ‘yan bindiga domin a dawo da dawwamammen zaman lafiya a yankin.
Matawalle ya ce luguden wutar da sojoji ke yi masu a yanzu, ya yi tsamarin da har ‘yan bindiga sun turo ‘yan aike, su na roƙon a yi sulhu tsakanin su da gwamnatin jiha.
Ya ce ‘yan aiken da ‘yan bindiga su ka tura masa sun shaida masa cewa sun tuba, sun daina garkuwa da kai hare-hare. Yanzu sulhu su ke nema su yi tsakanin su da gwamnati.
Ya ce a yanzu ‘yan bindiga masu yawan gaske sai arcewa su ke yi daga jihar Zamfara, sakamakon ruwan wutar da sojoji ke yi masu babu ƙaƙƙautawa.
Ya ce ‘yan siyasa su daina taimaka wa ‘yan bindiga ko ta wace hanya.
“Yan siyasa su ji tsoron Allah. Su daina sayen babura su na raba wa mutanen da ke sayarwa ga ‘yan bindiga su amfani da su wajen kai hare-hare.”
Matawalle ya ce Gwamnatin Jihar Zamfara za ta hukunta duk wani da aka samu ya na taimaka wa ‘yan bindiga, ko ya na sayen babura ana sayar masu.
Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta kafa tsauraran dokokin taƙaita safarar kayan abinci, fetur da dabbobi da kuma dakatar da cin kasuwannin mako-mako, duk domin a samu sauƙin hana kai wa mahara kayan abinci da toshe masu hanyoyin samun makamai da kuɗaɗe.