TARZOMAR SIYASA A KANO: Ƴan takife sun banka wuta a Hedikwatar APC ɓangaren Shekarau

Wasu masu zanga-zanga da aka yi wa mummunan zaton cewa magoya bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ne, sun banka wuta a Hedikwatar APC, ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

Hedikwatar ta su na kan titin Maiduguri, kusa da Barikin Mobal na Kano, a Hotoro, cikin Ƙaramar Hukumar Tarauni.

Rigima a tsakanin su ta taso bayan zaɓen shugabannin jam’iyya da ɓangarorin biyu su ka yi daban-daban a ranar 18 Ga Oktoba.

Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na APC ya ce ya amince da zaɓen shugaban APC ɓangaren Gwamna Ganduje, wato Abdullahi Abbas.

Ɓangaren Shekarau sun garzaya Babbar Kotun Tarayya, su ka nemi a soke zaɓen ɓangaren Ganduje, tun daga mazaɓu, ƙananan hukumomi da kuma jiha.

A ranar Talata kotu ta amince da wannan buƙata ta su. Bayan soke zaɓen ɓangaren Ganduje, kotu ta gargaɗe su kada su kuskura su sake wani zaɓe daban.

Wakilin mu ya gano cewa yayin da masu tarzoma su ka banka wuta, mutanen unguwa sun yi dandazo inda su ka yi kukan-kura suka fatattake su, sannan su ka taimaka suka kashe wutar.

Daga baya ‘yan sanda sun isa wurin bayan mutanen unguwa sun kashe wutar.

Wakilin mu bai samu jin ta bakin Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Kano ba.

Wannan tarzoma ta zo daidai lokacin da wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta haramta korar da Ganduje ya yi wa Murabus Sarki Muhammadu Sanusi II daga Kano, har kotun ta ci Kano tarar naira miliyan 10. Sannan kuma aka umarci Gwamnatin Kano ta nemi afuwar Sanusi a shafukan jaridu biyu.

Dama kuma a cikin Nuwamba Ganduje ya biya Ja’afar Ja’afar naira 800,000 da kotu ta ce ya biya shi, saboda ya ɓata masa lokaci a kotu.