TARON KAZAURE: Ƴan sanda sun fara farautan ɗan daban da ya luma wa ɗan APC wuka a ciki ya arce zuwa Kano

Mutum da ya rasa ransa a taron jami’iyyar APC da aka yi a karamar hukumar Kazaure jihar Jigawa ranar Talata.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Emmanuel Ekot wands ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES ya ce rundunar ta fara farautan dan daban da ya kashe mutumin.
“Mun samu labarin cewa wanda ya aikata wannan mummunar abu ya arce zuwa jihar Kano kuma mun fara farautar sa.
“Rikicin na cikin gida ne tsakanin magoya bayan ɗan takara da wasu ƴan jam’iyya ba rikicin jami’yya da jami’yya bane.
Gwamnan jihar Muhammad Badarau ne ya jagorancin taron jami’iyyar da aka yi a Kazaure ranar Talata inda a wannan wuri wasu ‘yan daba suka tada rikici har mutum daya ya rasa ransa.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa wanda aka kashe a taron na goyan bayan dan takaran sanata mai wakiltan Arewa maso Yamma a majalisar Dattawa mai suna Babangida Husseini.
Sunan wanda ya rasu a taron Halliru Lafka mazaunin Kazaure. Amma kuma bayan aukuwar lamarin mutane sun yi zanga-zanga inda suke zargin Husseini da laifin tara ‘yan daban da suka tada hankalin jama’a a garin.