Tabbas ‘yan bindiga sun sace matafiya da dama a titin Abuja-Kaduna, amma mun ceto mutum 11 cikin su – Kwamishina ‘Yan sandan Kaduna

Kwamishina ‘yan sandan jihar Kaduna Abdullahi Mudassiru ya tabbatar da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa Sagir Mudassiru, mai mallakin makaranta Famaks a titin Abuja – Kaduna.
Kwamishinan Mudassiru ya bayyana cewa ‘yan sanda tare da hadin guiwar sojoji sun ceto mutum 11 ciki har da gawar marigayi Hamida a kauyen Kurmin kare, dake iyaka da Titin.
Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya shaida wa manema labarai cewa rundunar ‘yan sandan jihar karkashin kwamishina Sagir Mudassir ta sanar masa cewa ‘yan sanda sun ceto mutum 11 da aka yi garkuwa da su a wannan hari.
Bayan haka ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro wajen ganin an kawo karshen hare-hare da ake kaiwa matafiya a wannan titi.
Hakazalika ya yi kira ga matafiya da su rika hakuri a lokacin da suke tafiya, su daina bin hannun da ba nasu ba domin hakan na sa a rika samun hadarurruka da kuma cunkoso a hanyar ta inda zai sa mugayen mutane su kawo wa matafiya hari.