TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su kai wa sojoji da mobal farmaki

Yayin da aka tabbatar da kisan mutum 43, waɗanda su ka haɗa da sojoji 30 da mobal 7, an kuma tabbatar da ɓacewar wasu jami’an tsaron a gumurzun su da ‘yan ta’adda a daji haƙar ma’adinan da ke Ajata-Aboki, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Mazauna yankin Shiroro a ranar Alhamis ce su ka shaida wa wakilin mu yadda ‘yan bindiga su ka yi wannan mummunar aika-aikar a ƙazamin harin da aka kai ranar Laraba.
Waɗanda su ka ga irin yawan zugar ‘yan ta’adda a kan babura ɗauke da zabga-zabgan makamai su ka ratattaki dandazon wurin da ake haƙar ma’adinan, su ka kashe farar hula, sojoji, mobal da kuma arcewa da wasu mutanen da su ka haɗa har da ‘yan ƙasar Chana.
Kakakin Gamayyar Ƙungiyoyin Raya Garin Shiroro mai suna Salisu Sabo, ya ce ba a yi zaton za a kai harin ba, saboda yankin ya shafe watanni ba a ji motsin an kai masa hari ba.
Ya ce su na zaune lafiya bayan da aka girke sojoji a yankin.
Sabo ya ce kafin ‘yan ta’addar su kai ga wurin haƙar ma’adinan, sai da su ka keta ƙauyuka da dama.
Sabo ya ce an ce maharan sun riƙa kwantar wa mazauna ƙauyukan hankula, su na ce masu kada wanda ya gudu, ba su aka zo kai wa hari ba.
An ce sun bindige wani mutumin ƙauye bayan sun tambaye shi hanyar da wurin haƙar ma’adinan, amma ya tsaya ya na yi masu dawurwura.
“Yan bindigar dai an tabbatar cewa Boko Haram/ISWAP ne. Da ganin su za ka san cewa ba ‘yan Najeriya ba ne. Su na da dogon gashin gashi a zai, ga kuma huda hancin su.
“Sun wuce su na ambaton Allah, Allahu Akbar!”
Sun rabu gida huɗu. Su na sanye da rigunan sojoji, ‘yan sanda, har da na ‘yan sakai.
“Su na isa ma’dinar kawai sai suka kwashi mutanen da su ka yi garkuwa da su, daga nan su ka buɗe wuta.”
“Da su ka isa Unguwar Maji da ke Mazaɓar Erena, a can ne su ka yi arangama da sojoji.
“Sojoji da maharan sun yi gumurzun da tun wajen 4 na yammaci, amma har washegari ranar Alhamis da safe mu na jin rugugin bindigu.”
Ya ce baya ga tulin jami’an tsaron da aka kashe, har yanzu wasu sun ɓace babu labarin su.
JIHAR NEJA TA KAMA WUTA: Mahara sun kashe sojoji 30, mobal 7, farar hula da dama, kuma sun arce da ‘yan Chana a wurin haƙar ma’adinai da ke Shiroro
ASHAFA MURNAI
Mummunan bayanin da ke fitowa daga Jihar Neja ya tabbatar da kisan aƙalla sojoji 30, ‘yan sandan mobal 7 da kuma farar hula da dama, a wani ƙazamin farmaki da mahara su ka kai wani wurin haƙar ma’adinai da ke cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da cewa an kai mummunan harin, kuma ta ƙara da cewa har yanzu ba ma tabbatar da ko adadin yawan waɗanda aka kashe ɗin ba.
Mazauna yankin da aka kai farmakin sun tabbatar da cewa sun waɗanda su ka fita tsintar gawarwaki baya ƙura ta lafa, sun ɗauko gawarwakin sojoji 30 da kuma da mobal 7 a cikin dajin da ke kewaye da wurin haƙar ma’adinan a safiyar Alhamis.
Haka kuma an tabbatar da kwaso gawarwakin fararen hula shida a cikin daji.
Mazauna yankin sun ƙara da cewa maharan sun kwashi mutane da dama ciki har da ‘yan Chana, su ka arce da su a ranar Laraba.
Wani jagoran matasa a Shiroro mai suna Yusuf Kokki, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mazauna yankin sun gani kuma sun ji lokacin da maharan ke wa wurin haƙar ma’adinan zabarin ruwan wuta da muggan makamai.
“A yanzu haka a kowane lokaci yawan waɗanda aka kashe a harin wanda aka kai Ajata-Aboki sai ƙaruwa ya ke yi. Domin zaman yanzu dai iyar gawarwakin da aka tsinto har da na sojoji 30 ne.”
Kokki ya ce ana sa ran ƙara gano wasu gawarwakin, saboda har zuwa safiyar ranar Alhamis masu ceto na ci gaba da neman gawarwaki a cikin jeji.
Ya ce maharan sun dira wurin haƙar ma’adinan, wadda mallakar wasu ‘yan Chana ce, inda su ka buɗe wa ma’aikata da masu tsaro wuta.
Ya ce tun a wurin haƙar ma’adinan take aka bindige mobal 7, da farar hula 6.
“Sojojin da aka girke a garin Erena su ka garzaya wurin domin kai ɗaukin gaggawa, inda ba su ankara sai mahara su ka afka masu da harbi, inda aka bindige sojojin Najeriya da dama.”
Da yawan waɗanda aka ji wa ciwo kuma an garzaya da su asibiti domin kula da su.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Neja, Emmanual Umar, ya ce artabun da aka yi da sojoji ya sa sojojin sun ceto jama’a da dama da hannun mahara.
Mahara sun kashe sojoji 30, mobal 7, farar hula da dama, kuma sun arce da ‘yan Chana a wurin haƙar ma’adinai da ke Shiroro.