SOKOTO: Yadda ‘yan bindiga suka saka wa duk gida harajin naira 2,500 a kauyen mu

Akalla mutum biyar ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyan Gatawa dake jihar Sokoto.
Hakan ya auku ne wata daya bayan ‘yan bindigan sun karbi Naira miliyan 11 kudin fansar mutum 20 da suka yi garkuwa da su a wasu kauyuka a jihar.
Gatawa kauye ne dake karkashin karamar hukumar Sabon Birni da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga babu kakkautawa a jihar Sokoto.
Wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunnan sa saboda tsaro ya ce maharan sun shigo kauyen da misalin karfe 8 na safen Larabar makon jiya.
” Basu kashe kowa ba amma sun gaya mana cewa kudi kawai suka bukata.
” Maharan sun aika da sakon cewa suna bukatar Naira 500,000 kudin fansar mutum biyar din da suka tafi da su.
“Maharan sun saka wa kauyen harajin Naira 2,500 akan kwani gida sannan za a hada kudin daga ranar Alhamis zuwa Litini wato yau.
“Mazaunan kauyen sun fara neman taimako daga wajen ‘yan uwa da abokan arziki da basu zama a kauyen domin su samu su biya harajin.
Bayan haka maharan sun kuma saka wa kauyen Tarah harajin Naira miliyan 7.
Wani mazaunin kauyen Usman Tarah ya ce haka kawai maharan suka saka musu harajin Naira milyan 7 ba tare da sun yi garkuwa da kowa ba.
Shima Mohammed Shehu mazaunin kauyen yace abin ya basu mamaki yadda maharan suka aiko da sakon a tara musu Naira miliyan 7 domin babu wani cikin nasu da maharan suka yi garkuwa da su.