Sojojin Najeriya shida sun ji rauni a wani gumurzu da Boko Haram ɓangaren ISWAP

Aƙalla sojojin Najeriya shida ne aka tabbatar cewa sun ji raunuka a wata arangama da su ka yi da ‘yan ta’addar Boko Haram, ɓangaren ‘yan ISWAP.

Wata majiya wadda ke da bayanin abin da ya faru, ta ce sojojin sun fita sintirin kakkaɓar ‘yan ta’adda ne a safiyar ranar Laraba a kewayen Burimari, wani ƙauye da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ngazai ta cikin Jihar Barno, a lokacin da su ka ji raunukan.

Daga nan aka gaggauta maida su a sansanin sojoji na garin Gajiran.

Wannan hari da aka kai wa sojojin ya zo ƙasa da sati ɗaya bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa sansanin sojoji a Zamfara, har su ka kashe wasu sojojin, su ka raunata wasu.

A harin na Zamfara dai an tabbatar da mutuwar sojoji 12 da kuma jikkata wasu sojojin su uku, wanda aka yi a Sansanin Sojoji da ke Mutumji, cikin yankin Ɗansadau.

Hare-haren na faruwa a lokacin da kuma a gefe ɗaya ake bada rahoton cewa daruruwan ‘yan ta’adda na miƙa wuya, su na yin saranda ga sojojin Najeriya.

Yayin da Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare, sau da dama Shugaba Muhammadu Buhari na ɗaukar alƙawari da shan alwashin daƙike matsalar tsaro a ƙasar nan.

A ciki wannan hali ne kuma ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da Sarkin Bunguɗu na Jihar Zamfara, wanda su ka kama a kan titin Kaduna zuwa Abuja.

An kuma tabbatar da rahoton ‘yan bindiga sun shiga ƙauyen su Kakakin Majalisar Zamfara, su ka ƙone gidaje da dama, ciki har da gidan Kakakin Majalisar na Zamfara.