Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ya roƙi Gwamnantin Tarayya ta ƙara wa alƙalai albashi

Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya, Monica Dongban-Mensem, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi wa alƙalai ƙarin albashi.

Monica wadda ta yi roƙon a wurin ƙaddamar da taron shekara na Kotun Ɗaukaka Ƙara na farko na 2021/2022, a Abuja a ranar Litinin, ta ce rabon da a yi wa alƙalai ƙarin albashi tun cikin 2007.

Ta nuna damuwa ganin yadda za a ce ana biyan Babban Jojin Najeriya (CJN) Naira 279,497 a matsayin albashin wata-wata. Yayin da manyan alƙalan Kotun Ƙoli ake biyan su Naira 206,425 kacal su ma.

Monica ta ce a matsayin ta na Babbar Mai Shari’a kuma Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Naira 206,425 ake biyan ta albashin wata-wata. Yayin da Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara ake biyan su Naira 166,285.

Yayin da ta ke kwatance tare da suna albashin su da na Alƙalan wasu ƙasashe, Monica ta ce albashin da ake biyan Alƙalan Najeriya cikin cokali ne, idan aka auna shi kan sikeli ɗaya da na wasu ƙasashe, har da wasu masu maƙwautaka da Najeriya.

Daga nan kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi su riƙe alƙawarin barin alƙalai da Majalisun Dokokin Jihohi su ci gashin kan su, kamar yadda Dokar Musamman ta 10 ta 2020 ta amince.

“Kusan shekaru sama da 10 kenan rabon da a yi mana ƙarin albashi.” Inji Monica, kuma ina roƙon a ƙara wa Kotun Ɗaukaka kuɗaɗen da ake bata, domin muna so mu fito da tsarin ingantawa da kirƙiro matakan sauƙaƙa batutuwa na yanke hukunci.” Inji Monica.