Shugaban Hukumar NITDA zai zama babban mai jawabi a taron Kamfanin Zuma Times

Zuma Times ta ziyarci shugaban hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) Malam Kashifu Inuwa Abdullahi a ofishinsa da ke shalkwatar hukumar a babban birnin tarayya Abuja.
Tawagar ƙaraƙshin jagorancin shugabar Kamfanin jaridar Hajiya Mairo Muhammad Mudi, ta ziyarci shugaban hukumar ne domin gabatar masa da takardar gayyata tare da neman ya kasance daga cikin masu jawabi a babban taron ta da za ta karrama fitatatun mutane ɗari cikin har da masu bibiyarta a Najeriya tare da gabatar da Kambun Girmamawa ga mutane 30 da ƙaddamar da Mujallar Kamfanin ta farko.
Taron zai gudana ne a ranar 25 ga watan Nuwamban 2021 a Abuja.

Shugaban Hukumar NITDA zai zama babban mai jawabi a taron Kamfanin Zuma Times
An kashe babban Kwamandan Boko Haram (ISWAP) Albarnawi

Da take gabatar masa da takardar gayyatar tare da takardar sheidar Zama daya daga cikin fitatatun Zuma Times 100, shugabar Kamfanin ta bayyana cewa Jaridar Zuma Times ta kasance mai yaɗa manufofi da ayyukan Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa tare da jinjina masa bisa jajircewa da kuma jagoranci na ban misali da yake gudanarwa a hukumar NITDA.
Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen taya shi murna a madadin shuwagabanni da ma’aikatan kamfanin ta na cika shekara biyu bisa kujerar shugabancin hukumar.
Daga Dama: Babban Direktan Hukumar NITD, Shugaban Kamfanin Zuma Times tare da Mawallafin Hausa Daily Times
Da ya ke mai da martani, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi ya bayyana farin ciki da ziyarar Kamfanin tare da godiya da gayyata da aka yi masa.
Ya bayyana cewa, hukumar NITDA a kullum tana maraba da ƙulla alaƙa da duk wani kamfani ko wata ƙungiya da aiyyukan su zai amfani al’umma tare da taimaka wa hukumar wurin cimma muradu da manufofin ta da ta saka a gaba.
Ya kuma bayyana cewa a shirye suke domin kulla alaƙa da Zuma Times wurin ƙara yaɗa kyawawan manufofin hukumar da kuma aiyyukan ci gaban ƙasa da suke gudanarwa.
Tawagar kamfanin ta samu tarba ta musamman daga shugaban hukumar tare da ma’aikatan ofishinsa.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 16, 2021 9:36 AM