Shin da gaske ne kotu a Najeriya ta umurci kamfanin MTN ya biya Mr Anenih naira miliyan 5.5? – Binciken DUBAWA

Zargi: Wani sakon WhatsApp na zargin wai kotun Najeriya ta umurci kamfanin MTN ya biya Emmanuel Anenih, wani mai amfani da layinta Naira miliyan 5.5 saboda wai kamfanin ya cire masa naira 50 ba tare da samun amincewarsa ba.

Wani sakon WhatsApp da aka yi ta yadawa a shafukan masu amfani da manhajar whatsapp na cewa wai wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih ya yi nasara a karar da ya shigar a kotu yana kalubalantar kamfanin MTN da cire masa naira 50 daga kudin kira da ya saka a layin sa na MTN cewa wai kudin wakar kira wanda shi bai amince da haka ba.

Sakamakon wannan sakon da yawa daga cikin masu amfani da manhajan whatsapp suka rika yin barazanar kama kamfanin a kotu cewa wai suma MTN na yi musu irin haka kamar yadda suka yi wa Mr Anenih.

Sakon na cewa “wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih ya kai kamfanin MTN kara kotu bayan da suka karya doka suka cire naira 50 cikin kudin da ya sayi kati ba da izinin sa ba. Babban kotun a Abuja ya samu MTN da laifi ya kuma umurci kamfanin ya biya Mr Emmanuek naira miliyan biyar..”

Wani mai amfani da WhasApp ne ya tambayi Dubawa ko za ta iya tantance gaskiyar wannan labarin.

Tantancewa

Da muka yi bincike a google, mun gano rahotannin da suka ambaci hukuncin kotun da aka yanke a watan Fabrairun 2020. Bayan da Emmanuel ya kai kamfanin MTN kotu a shekarar 2014 bayan da suka cire mi shi naira 50 ba da izinin sa ba.

Da muka yi karin bincike mun gano wani bidiyo mai tsawon minti biyu na wani labarin da aka sanya a tashar NTA. A cewar labarin, a watan oktoban 2014 Emmanuel Anenih ya kai MTN kotu bayan da suka zame kudi a wayarsa ba tare da izinin shi ba.

Bidiyon ya nuna cewa kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da wanda ya shigar da karar da kamfanin suka yi musayar sakonni dangane da batun. Haka nan kuma kotun ya ce akwai hujjojin da suka nuna rashin gaskiyar kamfanin tunda bayan da ya yi korafin, a daya daga cikin wasikun da kamfanin ya tura masa, akwai inda ya ambaci cewa lallai an cire kudin ba tare da izinin sa ba amma kuma sai suka aika ma sa kyautar naira 700 ladar shafe shekaru har 8 ya na amfani da layin na su.

NTA Ta ruwaito cewa a wannan shari’a babban alkalin kotun na birnin tarayyar a wancan lokacin, Ishaq cewa ya yi naira 700 bai kai diyyan irin matsalar da suka janyo mi shi ba. Dan haka alkalin ya umurci kamfanin ya biya miliyan biyar a matsayin diyya da wani karin dubu dari biyar a matsayin kudin da zai yi amfani da shi ya biya lauyoyi.

A Karshe

Wannan binciken ya nuna mana cewa da gaske ne kotun Najeirya ta umurci MTN ya biya Emmanuel Anenih naira milliyan biyar da rabi bayan da suka cire masa naira 50 a wayarsa ba tare da izinin shi ba.