Sama da ‘Yan ta’adda 13,000 da iyalan su suka mika wuya a jihar Barno

Hedikwatar tsaro ta kasa ta bayyana cewa zuwa yanzu ‘yan ta’adda 13,243 da iyalensu ne suka mika wuya Arewa Maso Gabashin kasar nan.

Mataimakin shugaban yada labarai na rundunar Bernard Onyeuko ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis da yake bayyana nasarorin da rundunar ta samu a fadin kasar nan.

Onyeuko ya ce daga cikin tubabbun akwai maza 3,343, mata 3,868 da yara kananan 6,234.

Ya ce rundunar Operation Hadin Kai ta samu wannan nasara a cikin makonni biyu ne saboda luguden wuta babu kakkautawa da ta sama da ƙasa da suka rika yi.

Onyeuko ya ce aman wuta da aka rika yi wa maharan ta sama da ƙasa a wurare daban daban a yankin Arewa maso Gabas ya taimaka wajen tarwatsa maharan da kama wasu daga cikinsu inda a ciki akwai masu kawo wa Boko Haram bayani game da gari da masu siyar musu da kaya.

Duk da haka wasu ‘yan Boko Haram din sun ajiye malamai sun mika wuya tare da iyalensu.

Gwoza – Yamtake – Bita road, Gwoza – Farm Centre – Yamtake road, tsaunin Mandara, Pulka da garuruwan Hambagda na daga cikin wuraren da dakarun sojojin suka ragargaza.

“A lissafe dai a cikin sati biyu dakarun sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 29, sun kama wasu ‘yan ta’adda 13 inda a ciki akwai masu kawo wa Boko Haram bayanai game da gari da masu siyar musu da kaya.

“Bindigogi 38, harsasan bindiga 968 da dabobbi 48 da aka sato na daga cikin kayan da sojojin suka kwato.

Onyeuko ya kuma ce dakarun sojojin sun buda wa kauyen Aulari dake Bama wuta inda suka konammotar bindiga uku, suka kashe ‘yan Boko Haram da dama sannan sauran sun gudu da raunin harsashi a jikin su.