Sako Zuwa Ga ‘Yan Uwana Hausawan Kasar Ebira! Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum,

‘Yan uwana masu albarka, masu daraja, kamar yadda kuka sani ne, Allah cikin ikon sa ya kaddari tun lokacin da Sarkin Hausawa na kasar Ebira (The Sarkin Hausawa of Ebiraland), Allah Yusuf Baba Sale, Allah ya karbi ransa (Allah yayi masa rahama, amin), muke ta kokarin bin al’amurran da suke faruwa, game da zabe da kuma nadin sabon Sarki, ba domin wata maslaha tamu ta kashin kan mu ba, a’a, sai dai domin maslahar al’ummar mu, da zaman lafiyar su, da hadin kan su!

Alhamdulillah, wasu sun bamu cikakken hadin kai da goyon baya da duk muke bukata, wasu kuma fandararru, musamman wadanda idon su ya rufe, masu neman matsayi, mulki da son girma ido rufe, sun dage akan sai sun tarwatsa hadin kai, da zaman lafiyar al’ummar Hausawan da ke rayuwa a kasar Ebira ta ko wane hali. Saboda su kamar yadda kowa ya sani, ba wani abu suke nema akan su samu wannan matsayi ba, illa suyi amfani da shi, suci gaba da zaluntar al’ummah, ko kuma su tara abun duniya!

Wallahi, wadannan mutane su sani, da ikon Allah, ba zamu taba zuba ido, muyi shiru, mu rungume hannuwa, muna kallo, har su jawo muna tashin hankali da fitina, saboda mugun son girman su ba. Da yardar Allah, zamu yaki duk wani shedani, mugu, azzalumi, wanda baya da manufa ta alkhairi ga al’ummar Hausawan kasar Ebira!!

Ya ku jama’ah, Ya ku al’ummar Hausawan kasar Ebira. Ku sani, muna da labarin cewa, wasu suna nan, suna yawo, suna yada cewa wai an zabe su a matsayin Sarkin Hausawa.

To muna sanar da ku cewa, wallahi, wallahi, wallahi, Allah shine shaida, babu wani mutum da aka zaba a matsayin Sarkin Hausawan kasar Ebira, har zuwa yau da nike wannan rubutu. Don haka, duk wani mutum da yake yawo, cikin gari, yana rudin al’ummah, yana cewa an zabe shi, ku sani, wannan mutum makaryaci ne, karya kawai yake yada wa, domin kawai ya raba kan al’ummah, kuma ya jawo muna tashin hankali da rudani tsakanin mu!

In Shaa Allahu, nan ba da dadewa ba, Allah zai yiwa al’ummah muwafaka, su zabi Sarkin su, wanda zai jagorance su, a matsayin Sarkin Hausawa, kuma wakilin Hausawa a kasar Ebira. Amma zuwa yanzu, babu wanda aka zaba a matsayin Sarki, ya kamata jama’ah su san da wannan!

Jama’ah ku sani, muna da cikakken labari cewa, akan wannan kujerar ta Sarkin Hausawan kasar Ebira, wallahi wasu suna nan suna raba kudi, wasu kuma sun kawo malaman tsibbu, da bokaye, da ‘yan bori, da matsafa, daga can arewa, wai suyi masu aiki, domin su samu wannan matsayi. To dukkanin su su sani, wallahi, da su da kudin nasu, da bokayen nasu, duk mun fi karfin su, domin mu Allah mu ka rike ba kowa ba, kuma ba wasu ba. Kuma su sani, duk wannan abun da suke yi, suna yi ne a banza, domin wannan matsayin, Allah Subhanahu wa Ta’ala, ya riga yasan waye za’a ba shi. Don haka shirme kawai suke yi, da bata lokacin su a banza a wofi!

Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah yasa mu dace, kuma Allah ya hada kawunan mu, kuma Allah ya dawwamar da mu akan zaman lafiya, amin.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi, Okene, Jihar Kogi, Najeriya. 08038289761.