Sakamakon gwaji ya nuna Abduljabbar ba shi da matsalar ƙwaƙwalwa

Asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa na Dawanau da ke jihar Kano ya ce Abduljabbar Nasiru Kabara ba shi da matsalar ƙwaƙwalwa.

A ci gaba da zaman sauraren ƙarar malamin da ake yi, duka lauyoyin Abduljabbar ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis.

An ruwaito cewa Lauyan Abduljabbar ɗaya ne ya halarci zaman kotun na yau Barista Haruna Magashi kuma take ya ce ya janye daga wakiltar malamin, BBC ta ruwaito.

  • Sakamakon gwaji ya nuna Abduljabbar ba shi da matsalar ƙwaƙwalwa
  • An kama waɗanda suka kashe ɗan Sanata Na’Allah da motarsa da suka sace a Nijar

Ya kuma ce “Sauran lauyoyin su ma sun janye daga kare Abduljabbar shi ya sa dukkansu babu wanda ya halarci zaman kotun.

A bayanin sakamakon gwajin asibitocin da aka gabatar wa kotun, Asibitin Dawanau na masu matsalar kwakwalwa ya ce an taɓa kwantar da Abduljabbar a asibitin na tsawon kwana huɗu a baya.

“Lokacin da ya taɓa yin rikici da ƴan uwansa an taɓa kwantar da shi a asibitin na kwana huɗu, amma ba a taɓa yi masa gwaji ba kuma ba a taɓa ba shi magani ba,” in ji mai karanto bayani a gaban kotun.

Alƙali Ibrahim Sarki Yola wanda ke yin shari’ar, ya tambayi sakamakon Asibitin Murtala da aka kai Abduljabbar domin yi masa gwajin kunne, saboda gaza amsa tambayoyin da aka yi masa a zaman kotun na baya, wanda ake tsammanin ko ya samu matsalar kunne ne.

“A sakamakon gwajin kunnen da muka samu daga Asibitin Murtala, an tabbatar da cewa Abduljabbar ba shi da matsalar kunne ko kuma ji ko kaɗan,” mai gabatar da bayani ya ce.

Alƙali Yola ya ce ya amince da buƙatar lauyoyin Abduljabbar na janye wa daga kare malamin.

An ɗage sauraren ƙarar Malamin zuwa ranar 30 ga watan Satumbar 2021.

An wallafa wannan Labari September 16, 2021 11:32 AM