Rundunar sojojin saman Najeriya ta ceto mutum 26 da aka yi garkuwa da su a Kaduna

A ranar Laraba ne Rundunar Sojin sama ta bayyana cewa ta ceto mutum 26 da aka yi garkuwa da su a Kaduna.

Kakakin rundunar Edward Gabkwet ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a Abuja.

Gabkwet ya ce sojojin sun ceto wadannan mutane yayin da suke sintiri a babban titin Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Ya ce bincike ya nuna cewa mutanen matafiya ne daga Birnin-Gwari zuwa Kaduna,wasu kuma daga Minna suke da jihar Kano.

“Mutanen sun bayyana wa sojojin cewa gungun masu garkuwa da mutane daban-daban har uku ne suka yi garkuwa da su.

“Masu garkuwa da mutanen sun gudu da wasu daga cikin mutanen da suka kama cikin daji bayan sun ji zuwan sojoji.

Zuwa yanzu rundunar ta kai mutanen asibiti domin likitoci su duba su inda daga nan za a mai da su jihohin su..

Gabkwet ya ce rundunar za ta ci gaba da farautar masu garkuwa da mutane domin ceto sauran mutanen dake hannun su.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a hanyar Zariya zuwa Kaduna.

A cikin mutanen da ‘yan bindigan suka kashe har da ɗan majalisan dake wakiltar Giwa a majalisar jihar, Honarabul Rilwanu Gadagau.

Wasu mazauna ƙauyukan da suka ga abinda ya auku sun bayyana cewa harin ya yi matukar muni domin duk wanda ya fara hannun ‘yan bindigan ko sun tafi da shi ko kuma ya mutu.

Hare-haren irin haka da ‘yan bindiga ke yi ya zama ruwan dare jihohin dake Arewa ta Tsakiya.

Jihohin Katsina, Zamfara da Neja na cikin jihohin dake fama da wannan matsala a Najeriya.