ROƘON BUHARI GA JIGA-JIGAN APC: ‘Kada ku bari APC ta afka cikin rikicin da ya fi na PDP muni’

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa uwar jam’iyya mai mulki APC wasiƙar gargaɗi da jan-hankalin yin kaffa-kaffa, kada jam’iyyar ta yi tashin gishirin Andurus.

Buhari ya yi gargaɗin ne biyo bayan yadda APC ta rikice kuma ta hargitse, yayin da zaɓen 2023 ke ƙara kusantowa.

Ya ce idan su ka bari rikici ya ci ƙarfin APC, to jam’iyyar ka iya ɓalɓalcewa kamar irin ɓalɓalcewar da PDP ta yi, har ta rasa mulki cikin 2015.

PDP ta yi mulki daga 1999 a jere, har zuwa 2015, inda rikici ya dabaibaye ta, APC ta ƙwace mulki a hannun ta, bayan ta shafe shekaru 16 ta na mulki.

Yanzu kuma rikici ya cumuimuye jam’iyyar APC tun ba ta ma cika shekaru 7 kan mulki ba, kuma yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa.

Ranar Litinin ce rikicin ya ƙara tsamari, inda Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja ya ayyana kan sa shugaban riƙon jam’iyya ba Gwamna Mala Buni na Yobe ba.

Gwamnonin Najeriya akasari sun mara masa baya, kuma sun zargi Buni da ƙoƙarin yi wa APC ƙafar-ungulu, ta yadda taron gangamin jam’iyya na ranar 26 Ga Maris a Abuja ba zai yiwu ba.

Shi kuwa Buhari, ya gargaɗe su cewa ahir, kuma su bi hankali, kada garin gyaran doro su karya ƙugu, ko gadon baya baki ɗaya.

APC ta daɗe cikin rikici tun kafin zaɓen 2019, wanda a lokacin sai da ta kai INEC ta hana jam’iyyar shiga zaɓen 2019 a jihohin Ribas da Zamfara.

Wani rikicin ya sa an tunɓuke tsohon shugaban APC Adams Oshiomhole daga kan kujerar sa, bayan rikicin sa Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya haddasa wa APC rasa Jihar Edo gaba ɗaya, har kujerar gwamna sukutum.

Bayan naɗa Mala Buni kan kujerar shugabancin riƙo, nan ma APC ba ta zauna lafiya ba, domin an riƙa Ƙalubalantar sa ana cewa shugabancin sa haramtacce ne, domin doka ta hana mai riƙe da wani muƙami ya riƙe shugabancin jam’iyya.

Har yanzu akwai ƙararrakin da aka gurfanar da shugabancin Buni a wasu kotuna.

A gargaɗin Buhari kuwa, ya kuma zargi kafafen yaɗa labarai da ruruta wutar rikicin shugabanci a APC.

Ya ce bai kamata kafafen yaɗa labarai su fi maida hankali wajen saɓanin shugabancin jam’iyya ba.

“Saboda shi shugaban jam’iyya ma fa da zarar zaɓe ya gabato, mantawa ake yi da shi, masu zaɓe sun fi maida hankali kan ‘yan takara, ba shugabannin jam’iyya ba.”