ROƘON A SAKI NNAMDI KANU: Yadda dattawan ƙabilar Igbo su ka faɗi ba nauyi, su ka tashi ba nauyi a gaban Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa wasu dattawan ƙabilar Igbo cewa ba zai shiga hurumin ɓangaren shari’a ba, domin ya saki Nnamdi Kanu, wanda a yanzu batun tuhumar da ake masa na kotu.

Buhari ya yi wannan furucin ne yayin wa wasu gungun manyan dattawan ƙabilar Igbo su ka kai masa ziyarar roƙon ya saki Nnamdi Kanu da ke tsare.

Nnamdi Kanu, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya ko da tsiya, ya shiga hannun hukuma ne yayin da aka kamo shi daga waje, bayan ya tsallake ƙasar nan daga belin sa da aka bayar.

Shugaban tawagar mai suna Mbazulike Amaechi, ya shaida wa Buhari cewa sun zo ne domin su roƙe shi alfarmar ya saki Nnamdi Kanu domin a samu zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

Mbazulike, wanda dattijo ne mai shekaru 93 a duniya, ya shaida wa Buhari cewa a cikin ministocin da aka yi a Jamhuriya ta ɗaya, shi kaɗai ne ya rage a duniya.

“Ina roƙon Shugaban Ƙasa ya yi alfarmar cewa idan ya saki Kanu, ni da kai na zan sa masa takunkumin hana shi yin irin kalaman ɓatuncin da ya ke yi.

“Na kasance dattijon da ake girmamawa a Yankin Kudu maso Gabas sosai. Ina roƙon a ba ni shi domin dama ce ta samar da zaman lafiya a yankin mu.

“Ya mai girma Shugaban Ƙasa, yankin mu ya shiga cikin gagarimar matsala saboda tashe-tashen hankulan da ake yi dalilin IPOB.

“Harkokin tattalin arziki sai ja baya su ke yi. Ga kuma harkar ilmi ta shiga garari. Matsalar tsaro kuma sai ƙara ƙamari ta ke yi.

“Na yi amanna da cewa a bi matakin diflomasiyyar siyasar cikin gida a wanzar da zaman lafiya a yankin shi ne mafi alheri, ba amfani da ƙarfin soja ba.

“Ba zan yi fatan na mutu na bar yankin mu cikin tashin hankalin da ya ke ciki ba a yanzu.

“Shugaban Ƙasa wannan dama ce gare ka cewa idan ka saki Kanu, ka zama shugaban da ya samu yankin mu ciki rikici, amma ya wanzar da zaman lafiya a yankin.”

Jawabin Buhari Ga Dattawan Ƙabilar Igbo Masu Roƙon Ya Saki Nnamdi Kanu:

Buhari ya shaida wa Mbazulike cewa ba zai so ya shiga hurumin ɓangarorin gwamnati ba, domin fannin Shari’a ba ɓangaren sa ba ne.

“Na tabbata babu wanda zai iya fitowa ya ce a tsawon shekaru shida da na yi a kan mulki, na yi wa ɓangaren Shari’a katsalandan ko sau ɗaya.

“Da farko dai ina jinjina maka a matsayin ka na dattijo wanda ya haura shekaru 90, amma kaifin tunanin ka garau ya ke. A yanzu haka akwai masu rabin shekarun ka a duniya, amma idan su na magana, ba su iya kama-tasha.

“Kuma ina yi maka ta’aziyyar mutuwar matar ka, wadda ta bar duniya kwanan nan.

Batun Kanu kuwa abu ne mai matuƙar wahalar da zan sa baki a kai. Amma zan duba na ga mai iya yiwuwa.

“Lokacin da ya tsare daga belin da aka bayar na shi, da aka kamo shi aka dawo da shi. Ai gata mu ka yi masa da muka ce idan
ya na da wata jayayya, ya tafi kotu.”

Mbazulike ya sha wa Buhari alwashin cewa sakin Nnamdi zai samar da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

“Ni ba ni goyon bayan IPOB, ina ƙaunar kasancewar Najeriya dunƙulalliyar ƙasa ɗaya.”

Tawagar dai ta mutum shida ce, ciki kuwa har da Chukwumeka Ezeife.