RIKICIN RASHA DA UKRANIYA: Kowa ya yi tanadi, za a yi tsananin karancin abinci nan da watanni biyu masu zuwa a Najeriya- Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya gargadi yan Najeriya cewa kowa yayi tanadi kuma a kwana shirin tsindumawa cikin matsanancin karancin abinci da tsananin yunwa a kasar nan nan da watanni biyu masu zuwa.

Dangote ya ce dole gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci, masana;antu da noma su zauna a tattauna yadda za akawo karshen wannan matsala da ya tunkaro mu tunda wuri domin babu makawa sai ta iske mu.

Ya kara da cewa tun yanzu an fara samun hauhawan farashin abubuwa a kamar Taki, Masara, Alkama da dai sauran su.

” Za a samu karancin Masara da alkama a duniya saboda yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraniya. Wadannan kasashe sune ke samar da kashi 30 cikin 100 na uria da ake yin takin zamani da shi.

” Za a samu matsalar karancin abinci matuka. Ba za mu iya samun taki ba amma kuma ba za mu ga illar ba yanzu sai nan da watanni biyu zuwa uku masu zuwa. Ita kanta Amurka zata ji a jiki.

” Yanzu mutane na siyar da masara zuwa kasashen waje saboda daraja da ta yi. Wannan babban hatsari ne. Dole a hana su tunda wuri sannan a kirkiro hanyoyin da za mu yi noma da gasken gaske a kasarnan domin kowa ne fa zai dandana kudar sa.

Haka nan shima shugaban kamfanin sarrafa filawa floor Mill Boye Olusanya ya bayyana cewa tun yanzu an fara samun hauhawan farashin kayan abinci.

Ukraniya na daga cikin kasashen duniya dake noma masara da yawan gaske. yakin Rasha ya sa ana samun karancin masara wanda shine ya musanya alkama.