RASHIN TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 15 a makon jiya a Najeriya

Akalla mutum 15 ne ‘yan bindiga suka kashe a makon jiya wato daga ranar 7 zuwa 13 ga Agusta.
Najeriya ta samu raguwa a wayan mutanen da aka kashe a makon jiya idan aka kwatanta da wadanda aka kashe a makon baya.
Daga cikin mutum 15 din da aka kashe mutum 14 mutanen gari ne, mutum daya kuma ma’aikacin hukumar shiga da fice ta ƙasa ne.
Jihar Taraba
‘Yan bindiga sun kashe mutum uku a garin Bali dake karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
Maharan sun kuma sace mutane da dama.
Jihar Jigawa
A karamar hukumar Maigatari dake jihar Jigawa ‘yan bindiga sun kashe ma’aikacin hukumar shige da fice ta ƙasa sannan wasu mutum biyu sun ji rauni.
Maigatari gari ne dake kusa da kasar Niger.
Jihar Benue
‘Yan bindiga wanda ake zargin makiyaya sun kashe mutum 6 a kauyukan Tse Ngojov da Tse Valem Yaweh dake karamar hukumar Logo.
Jihar Kwara
Mutum hudu sun rasu a wajen wani taro inda ‘yan kungiyar Odua People’s congress suka yi arangama da wasu fulani makiyay.Jihar Ekiti
‘Yan bindiga sun kashe wani dan achaba mai suna Abejide Ojo ranar Alhamis dinmakon jiya a hanyar Ilemeso zuwa Isan zuwa Ekiti a jihar Ekiti.