RASHIN TSARO: Gwamnatin Kaduna ta sanar da bude hanyoyin sadarwar waya a kananan hukumomin da ta toshe

Duk da ci gaba da samun tsananin rashin tsaro a jihar Kaduna da ake fama dashi, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da bude hanyoyin sadarwa a kananan hukumomin da ta toshe a watan Oktoba.

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da haka ranar Juma’a a garin Kaduna.

Aruwan ya ce tuni gwamnati umarci hukumar sadarwa ta kasa ta bude hanyoyin sadarwa da ta dakile tun a watan Oktoba sai dai har yanzu dokar hana cin Kasuwanni mako-mako da aka dakatar na nan.

Aruwan ya kara da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da tsaro a jihar da kuma gamawa da yan bindiga da suka addabi jihar.

Idan ba a manta ba, gwamnatin Kaduna ta sanar da toshe hanyoyin sadarwar wayar tarho da kuma dakatar da wasu kasuwannin mako mako da ake ci.