Rashin samun barci akalla na awa biyar na toshe jijiyoyin dake daukan jini a jikin mutum – Binciken Likitoci

Sakamakon bincike da aka gudanar ya nuna cewa mutanen dake samun barci kasa da sa’o’i biyar a dare na cikin hadarin kashi 74% na samun matsalar toshewar jijiyoyin jiki dake daukan jini.

Kwararrun jami’an lafiya kan cututtukan dake kama zuciya na kasashen turai ESC ne suka gudanar da binciken wanda aka wallafa sakamakon binciken a shafin kungiyar ‘European Society of Cardiology (ESC)’ dake yanar gizo ranar Alhamis.

Jagoran masu binciken Shuai Yuan ma’aikacin asibitin Karolinska dake Stockholm a Sweden ya ce samun barci akalla na tsawon sa’o’I 7 zuwa 8 na daga cikin hanyoyin dake taimakawa wajen rage kamuwa da cutar toshewar jijiyan dake daukar jini a jikin mutum.

Yuan ya ce zuwa yanzu mutum sama da miliyan 200 na dauke da cutar a duniya inda jini baya iya wucewa ta kafa wanda hakan ke kawo cututtukan bugawar zuciya da shanyewar bangaren jiki.

“Rashin samun isasshen barci na daga cikin matsalolin da mutanen dake dauke da wannan cuta suka fi kokawa da shi.

“Binciken ya gano cewa akwai gibi kan yadda barci ke haddasa wannan cutar da yadda cutar ke iya hana mutum samun isasshen barci.

Yuan ya ce rashin motsa jiki na daga cikin matsalolin dake kawo cutar a jikin mutum.

Likitan ya yi kira ga mutanen dake fama da wannan cuta cewa rage radadin ciwon da cutar ke sakawa a jikin mutum na daga cikin dabarun da zasu taimaka musu wajen samun isasshen barci.