Rashin kula, shan duka suka sa nake so a raba ni da mijina – Tawakalitu a Kotu

Wata mata ‘yar kasuwa Tawakalitu Olayiwola ta kai karar mijinta Ganiu Olayiwola kotu dake Mapo Grade A a Ibadan domin ta raba auren ta na shekara 20 saboda rashin kula da mijinta baya yi mata.
Tawakalitu mahaifiyar ‘ya’ya uku ta bayyana cewa a dalilin zama da Ganiu ta kamu da ciwon hawan jini baya ga rashin kula da dan karan duka da take sha a hannun sa.
Ta ce Ganiu baya kula da su iyalansa domin Naira 1,000 kacal yake badawa kudin abinci da cefane duk wata 6.
“A dalilin haka ya sa na fara sana’a domin kula da kai na da ya’ya na. Saboda haka ya sa nima bana iya saduwa da shi domin hidimomi sun yi min yawa, idan na dawo gida sai barci.
“A dalilin haka ya sa Ganiu ya fara yi min kazafin wai ina karuwanci a waje, sai ya tirke ni ya yi ta lakaɗa min duka sannan kuma har da watsa min ruwan batir a fuska.
Tawakalitu ta ce Ganiu na yi mata sata domin wata rana ya saci talabijin da wayar ta inda ko da ta kai shi kara ofishin ‘yan sanda ya musanta haka.
Ganiu ya goyi bayan kotu ta raba auren musamman yadda Tawakalitu ta daina saduwa da shi da yadda take yawan dawowa gida da dare.
“Shekara uku kenan nake jan kunnen Tawakalitu kan yadda take dawowa gida da dare amma ta ki dainawa inda hakan ya sa nake dukan ta.