RANAR YAƘI DA FATARA DA YUNWA A DUNIYA: Attajirai 22 na duniya sun nunka matan Afrika kuɗi sau biyu -UN

Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Gutteres ya bayyana cewa akwai alhaki da rashin tausayi ga masu hali, ganin yadda miliyoyin mutane ke ƙara faɗawa cikin yunwa da fatara da talauci a duniya.

Da ya ke bayani a a Ranar Jimamin Yaƙi da Fatara da Yunwa a Duniya, wato ranar 17 Ga October, Gutteres ya ce abin takaici ne a ce a cikin shekarar 2020 mutum fiye da miliyan 120 sun afka cikin ƙuncin fatara, yunwa da talauci a duniya.

Ya nuna damuwa dangane da yadda ake ƙara samun rata da tazara mai yawa tsakanin masu hali da faƙirai da matalauta.

“A yayin da mu ke yaƙin ganin an kawar da yunwa a duniya, to kuma wajibin mu ne mu ga an rage rata da tazarar da ke tsakanin masu hali da matalauta.

“Annobar korona ta jefa aƙalla mutum miliyan 120 cikin ƙuncin rayuwa a duniya. Haka nan kuma yadda ake samun fifikon wadatar rigakafin korona a wasu nahiyar fiye da wata nahiyar, shi ma ya ƙara bazuwar cutar a inda babu wadatar makarai da riga-kafi sosai.

“Ko kafin ɓarkewar cutar korona, dukiyar manyan attajiran duniya su 22, ta zarce yawan dukiyar da matan Afrika arankatakaf su ka mallaka.”

Gutteres ya ce idan mutum ya ƙara da cewa rata da tazarar da ke tsakanin mai hali da faƙiri sai ƙara faɗaɗa ta ke yi.

Ya jaddada ƙudirin Hukumar UNDP na fitar da mutum miliyan 100 daga cikin fatara da yunwa tsakanin 2022 zuwa 2025.