RAHOTON MUSAMMAN: Hijirar Kwamandojin ‘Yan Bindiga daga Zamfara zuwa dajin Sokoto

Watanni kaɗan bayan Gogarma Bello Turji da kwamandojin sa sun tashi daga dajin Zurmi a jihar Zamfara, sun kafa hedikwata a dajin Sakoto tsakanin Isa da Sabon Birni, yanzu kuma PREMIUM TIMES ta binciko cewa shima hatsabibin nan Halilu Sububu, wanda aka fi sani da Halilu ‘Roket’, ya kwashe ta sa rundunar daga dajin Sububu a cikin Karamar Hukumar Shinkafi, ya tsallaka cikin Jihar Sokoto, ya yi na sa sansani kusa da na Bello Turji.

Halilu kamar yadda binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar, shi ma yanzu ya kafa sansani a kusa da ƙauyen Gwalama bayan garin Suruddubu, cikin dajin da Turji ya yi na sa sansanin, a cikin Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto.

Halilu Sububu hatsabibin Bafulatani ne maras tausayi. Majiya ta tabbatar da cewa shi ne ya yi garkuwa da ɗalibai da malaman Kwalejin Koyon Aikin Noma ta Bakura, kuma shi ne ya kwashe sama da mutum 80 a garin Gora Namaye, cikin Ƙaramar Hukumar Maradun duk a jihar Zamfara.

Halilu ‘Roket’: Haihuwar Mugun Iri A Sububu: Halilu haifaffen Sububu ne, kuma a can ya tashi, cikin Ƙaramar Hukumar Shinkafi a jihar Sokoto.

Fitinannen hatsabibin gaske ne. Shi ne kwamandan da ya raini Bello Turji kuma ya sallame shi bayan shi ma ya zama gagararre. A yanzu ma ana ganin Turji ya fi ogan sa Halilu ‘Roket’ masifa.

Halilu ‘Roket’ aminin fitinannen dillalin bindigogi ne mai suna Shehu Rekeb.

Tuni an haɗe da Halilu da Turji da dillalin manyan bindigogi Shehu Rekeb. Kuma dukkan su Fulani ne, ‘yan asalin jihar Zamfara.

Dajin Sububu ya yi iyaka da Ƙananan Hukumomin Maradun, Shinkafi, Bakura, Talata Mafara a Jihar Zamfara.

Shi ne kuma ya mazaya har cikin Jihar Sokoto, inda ya yi iyaka da ƙananan hukumomin Raɓa, Tureta, Isa da Goronyo.

Jami’an tsaron sirri na ganin an haɗa kai ne tsakanin manyan kwamandojin ‘yan bindiga ɗin domin sake wani gagarimin shirin ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna.

Sojojin Najeriya sun nuna cewa hare-haren da aka riƙa kai masu ba ƙaƙƙautawa a jihar Zamfara ne ya sa su ka gudu zuwa cikin jihar Sokoto.

Wani mai suna Basharu Guyawa da ke bibiyar ayyukan ‘yan bindiga, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Halilu da sauran sun guje wa farmakin da sojoji ke yi masu ne a Zamfara.

Ya ce amma kuma a yanzu su ukun duk sun ƙulla harkokin su wuri ɗaya. “Kuma hakan da su ka yi zai ba su damar shiga har cikin Jamhuriyar Nijar su ɓoye idan sojojin Najeriya sun kai masu farmaki. Tunda dajin da su ke a yanzu, ya yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“Har yanzu haka Halilu ‘Roket’ na zuwa ƙauyen su Sububu, sannan ya koma cikin daji a sansanin sa.” Inji wata majiya da ta tabbatar da hakan da ke zaune a ƙauyen Galadi.

An kuma tabbatar cewa harin da aka kai wa wani sansanin sojoji watanni biyu da suka gabata a Sokoto, taron-dangi ne aka yi tsakanin ɓangaren Halilu ‘Roket’, Bello Turji da kuma Shehu Rekeb.

Gogarma Bello Turji: Gagarau Mai Jiran Daga:

Yadda Gogarman ‘yan bindiga Turji ya fice daga dajin Zurmi, ya kafa hedikwata a yankin Isa a Sokoto.

Matashin gogarman ‘yan bindiga Turji, ya yi gaba da rundunar sa daga dajin Zurmi cikin Jihar Zamfara zuwa yankin Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto.

Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Turji, ya bar dajin Fakai cikin Karamar Hukumar Zurmi tun kafin sojoji su fara ragargazar dajin da ya yi sansani shi da yaran sa.

Haka dai wata ƙwaƙƙwarar majiya ta sanar da PREMIUM TIMES.

Sau da dama ya na yin fatali da ƙoƙarin yin sulhu da Gwamnatin Jihar Zamfara.

Sau ɗaya ne ya ce a shirye ya ke a yi sulhu da shi, wato a lokacin da Sheikh Ahmed Gumi ya kai masa ziyara a sansanin sa, a Zurmi cikin Jihar Zamfara.

Kusan tsawon watanni biyu kenan Turji ya na riƙe da mahaifin Kakakin Majalisar Jihar Zamfara, kawun kakakin da kishiyar mahaifiyar kakakin, waɗanda ya tura yaran sa su ka kamo masa su a ƙauyen Magarya, mahaifar Kakakin Majalisar Zamfara, Nasiru Magarya.

PREMIUM TIMES ta buga yadda wani kwamandan Turji mai suna Ɗan Bukkolo ya shaida wa masu kai kuɗin fansa cewa Turji ya ce su koma da kuɗin su, ya fasa sakin mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara ɗin da sauran dangin sa da ya ke riƙe.

Hijirar Turji Daga Zamfara Zuwa Isa A Sokoto:

Majiyoyi daga sassa daban-daban, har da cikin jami’an tsaro sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Turji ya kafa hedikwata tsakanin dajin Tozai da Suruddubu cikin Ƙaramar Hukumar Isa, a Jihar Sokoto.

“Turji ya kafa hedikwata kilomita huɗu bayan an wuce ƙauyen Tozai kafin a kai ƙauyen Suruddubu.” Inji wata majiya.

Shugaban Ƙungiyar Rundunar Adalci ta Jihar Sokoto, Bashir Altine, ya ce ya yi amanna cewa Turji ya gudo ne daga Fakai zuwa Tozai da Suruddubu domin ya kauce wa ruwan hare-haren da sojoji ke kaiwa.”

Altine ya ce matakan da Jihar Zamfara ke ɗauka a yanzu ya na shafar su sosai.

Ya ƙara da cewa al’ummar Tozai da Suruddubu da kewayen su babu abin da za su iya yi.

“Yanzu zai iya kai hare-haren a Isa da Isa ta Arewa kan sa tsaye babu mai iya tare masa hanya.” Inji Altine.

Majiya a cikin jami’an tsaron Katsina sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga da dama na ta canja wurin kafa sabbin sansanonin su.

Akwai Wata Tsiyar Da Turji Ke Ƙullawa:

Wata majiya daga Sabon Birni, da ke zaune a Sokoto, ta shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa ba mamaki akwai wata tsiyar da Turji ke ƙullawa ko shiryawa, shi sa ya kafa hedikwata tsakanin Tozai da Suruddubu a Jihar Sokoto.

“Idan ka lura, Turji ya shirya da gogarman ‘yan bindigar yankin Shinkafi da Sabon Birni, Halilu Sububu. Kai ko babu taimakon Halilu da yaran sa, Turji zai iya kai wa kowane ƙauye hari.”

Majiya ta ce yaran Turji da na Halilu ne su ka kai wa sojoji mummunan hari a yankin Dama.

“Turji ne da kan sa ya jagoranci kai harin. Saboda ya sha aika wa mazauna yankin wasiƙar cewa ya gano su na kai wa jami’an sojoji rahoto kan Turji ɗin. Kuma ya sha aika saƙo ga sojoji da sauran jami’an tsaro, ya na gaya masu cewa zai kai hari, kuma harin da zai kai, zai yi muni sosai.”

Dama Sanata Ibrahim Gobir ya shaida wa Zauren Majalisar Dattawa cewa ‘yan bindiga sun tare a yankin mazaɓar sa, saboda a can babu yawan sojoji masu kai masu hare-hare.