RAHOTO: Akalla ‘ƴan Najeriya miliyan 48 ne ke ƙantara kashi ‘bahaya’ a waje

Sakamon binciken da WASH-NORM ta gudanar a shekaran 2021 ya nuna cewa har yanzu akwai ‘yan Najeriya miliyan 48 dake kantara bahaya a waje.
An gabatar da wannan rahoto a Abuja ranar Talata.
Ministan ruwa Suleiman Adamu ya ce har yanzu mutane na wahalan samun tsaftataccen ruwa da rashin tsaftace muhalli saboda yawan da ake kara yi sannan da cutar Korona da aka yi fama da shi.
An kirkiro WASH-NORM domin gudanar da bincike kan yadda za a shawo kan matsalar rashin ruwa da tsaftace muhalli a kasar nan.
Sakamakon da WASH-NORM ya gano zai taimama wa gwamnati wajen daukar matakan da za su taimaka wajen kawo karshen matsalar.
Rahoton ya kuma nuna cewa matsalar yin bahaya a waje ya fi yawa a yankin karkara fiye da birane.