RA’AYIN PREMIUM TIMES: FAƊUWAR DARAJAR NAIRA: CBN ya saki jaki, ya koma dukan taiki

Wata tara cur kenan a duk lokacin da Naira ta shiga gasar kokawa da kuɗaɗen waje a tsakiyar kasuwa, sai an tandara ta a ƙasa. Lamarin ya kai ta kwance, har ta na neman kasa tashi. An yi kirari, an kambama ta, an jinjina mata ganga, amma ko sau ɗaya ba ta taɓa kayar da dala a ƙasa ba.

Idan aka dubi wannan lamari kafin a yi bincike mai zurfi, za a iya cewa hukuncin da Babban Bankin Najeriya, CBN ya ɗauka, inda ya dira kan shafin yanar gizo na abokifx.com, wanda ke buga farashin Naira da dala da sauran manyan kuɗaɗen waje a kasuwar ‘yan canji, abu ne mai kyau.

Yin duba da CBN ya daina sayar da dala a ‘yan canji, abu ne da ake ganin babban bankin ya ɗauko matakan sharewa ko shafe kasuwar ‘yan canji baki ɗaya, ko kuma tsaftace hada-hadar.

Sai dai kuma irin yadda Naira ke shan dukan tsiya a filin dambe da kuɗaɗen ƙasashen waje, abu ne mai tayar da hankali, bisa la’akari da cewa a yanzu ne tattalin arzikin Najeriya ke ƙoƙarin fita daga ƙangi da ƙuncin da ya shiga tun bayan ɓarkewar cutar korona a duniya.

Sannan kuma ana cikin mawuyacin halin da Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta kafa ƙa’idar rage adadin ɗanyen man da kowace ƙasa ke haƙowa.

Wannan ƙa’ida kuwa ta rage wa Najeriya samun kuɗaɗen shiga, domin bayan kafa ƙa’idar, farashin litar ɗanyen mai ta yi daraja a duniya.

A wannan lokacin kuma an fuskanci raguwar maƙudan kuɗaɗen Najeriya da ke asusun ajiyar ta na waje.

Wata kiki-kakar kuma ita ce, maimakon a riƙa samun kwararowar masu shigowa Najeriya da maƙudan daloli su na zuba jari, sai ya kasance babu inda wani mai zuba jari ko wata babbar hada-hada zai iya samun canjin kuɗaɗen waje a ƙasar nan, sai a CBN.

Ai kuwa tunda har ba a samun wadatar daloli ko kuɗaɗen waje sosai, to akwai gagarimar matsalar tsadar komai kenan. Sai aka yi mummunan katarin yadda CBN ta ƙara farashin kuɗin ruwa ga masu karɓar ramce.

Wannan ya haifar da tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki, ta yadda babu wani abu da masu zuba jari ko a nan cikin gida za su iya yi domin samun riba.

Dalili kenan masu abin hannun su, su ka maida hankali wajen sayen kadarori, gina maka-makan rukunin gidaje, hada-hadar ‘bitcoin’ wato ‘cryptocurrency’ da sauran su.

Wannan lamari ya karya darajar Naira ta na neman komawa martaba ɗaya da karan taba sigari, ko kuma daraja ɗaya da soson wanke-wanke.

A wannan yanayi, ba lallai ba ne a ce wai abokifx.com ya iya juya akalar darajar Naira a kasuwar canji domin amfanar kan sa. Saboda ne, ba zai iya ƙara wa kaya kuɗi ko rage masa farashi a kasuwa ba.

Saboda haka PREMIUM TIMES ta haƙƙaƙe cewa ba daidai ba ne a ce a danne abokifx.com ko a tauye masa haƙƙin sanar da bayanai a matsayin sa na kafar sadarwa ba.