QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

Walid dai shi ne kociya ɗan Afrika na farko, wanda ya fara kaiwa wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, wato kwata fainal.

An naɗa Walid Regragui, wanda ke horas da ‘yan wasan Morocco a cikin watan Agusta, bayan ya kai ƙungiyar da ya ke horaswa, wato Wydad Casablanca FC kaiwa ga nasarar lashe Kofin Zakarun Afrika.

Tun daga lokacin da ya karɓi jan ragamar ƙungiyar ƙwallon ƙafar Morocco, wato Atlas Lions, har yau ƙwallo ɗaya kaɗai aka saka masu a raga a cikin wasanni bakwai da su ka yi, waɗanda huɗu a gasar Qatar 2023 ta yi su.

Morocco ta lashe Chile da ci 2-0, ta yi kunnen-doki 0-0 da Paraguay, ta lallasa Georgia da ci 3-0, ta yi kunnen-doki 0-0 da Croatia, ta ci Belgium 2:0.

Belgium ce ƙasa ta biyu a duniya a jerin ƙasashen da ke da ƙarfi a ƙwallon ƙafa. Amma hakan bai hana Morocco lallasa su ba. Tuni an kore su daga Qatar, sun koma gida.

Morocco ta ci Canada 2-1, sannan ta fitar da Spain da bugun fanereti, 3:0.

Ba a Morocco kaɗai aka yi ta murna da nasarar da ƙasar ta yi a kan Spain ba. Kusan dukkan ƙasashen Larabawa, Afrika, Portugal har da wasu a Isra’ila duk an yi murna.

A Spain, dubban ‘yan Morocco sun fito kan titin birnin Barcelona su na kaɗe-kaɗe da raye-raye, tare da buga batoyi mai launin ja saboda murna.