QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

A daidai lokacin da Croatia ta yi nasara kan Brazil a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a ranar Juma’a, ƙididdigar yawan al’ummar Croatia su 4,043,819 ne. Wato ba su ma kai al’ummar Jihar Jigawa a Najeriya yawa ba.

A dai lokacin ƙasar Brazil yawan jama’ar ta su 216,280,879 ne. Wato dai Brazil ta nunka Croatia yawan jama’a aƙalla sau 40.

Croatia ta fitar da Brazil a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan sun yi 1:1 a ƙarin lokacin mintina 30 da aka ba su.

Wannan ne karo na 3 da Croatia ta kai wasan kusa da ƙarshe, kuma wannan ne karo na 2 da kai wasan kusa da na ƙarshe a jere.

Rabon da wata ƙasa ta mai wasan kusa da na ƙarshe sau biyu a jere, tun Brazil a 1998.

Croatia dai idan ba a manta ba, ta kai wasan ƙarshe a RASHA 2018.

Yanzu dai Croatia za ta haɗu da wanda ya yi nasara tsakanin Argentina da Natherland.

Croatia ta samu ‘yancin ta cikin 2002, bayan ta ɓalle daga Yugoslavia.