QATAR 2022: Samuel Eto’o Ya Yi Nadama Game Da Hatsaniya A Wajen Gasar Cin Kofin Duniya

Shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru kuma tsohon dan wasan kwallon kafa Samuel Eto’o ya nemi afuwar wani mutum da ya ture kasa a wani abin da ya kira ‘mummunar hatsaniya’ a wajen wani filin wasa na gasar cin kofin duniya da safiyar Talata.