QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

A ci gaba da gasar cin Kofin Duniya na Qatar 2022, cikin kartsetsiyar ranar Talata Saudiya ta kafa tarihin lallasa Ajentina da ci 2:1 a wasan Rukunin C.

Wannan nasara ce wadda tarihi ne wanda rabon da a taɓa yin irin haka, tun nasarar da Senegal ta samu a kan Faransa a zagayen farko na rukunin gasar cin Kofin Duniya.

Wannan nasara ta karya tutiya da tinƙahon da Ajentina ke yi, domin kafin ta sha kashi a hannun Saudiyya, su Messi sun jera wasanni 36 a jere babu wata ƙasa da ta yi nasara a kan su.

Messi ne ya fara zura wa ragar Saudiyya ƙwallo ta hanyar bugun fenariti, daidai minti 10 da fara wasa.

Sai dai kuma Al Shehri na Saudiyya ya guma wa Ajentina sharri, inda ya rama cin da aka yi masu, daidai minti na 48, wato minti uku bayan dawowa daga rabin lokaci.

A minti na 53 ne kuma Al Dawsari ya danƙara wa Ajentina ƙwallo ta 2, wadda har aka tashi Ajentina su ka kasa yin ko da kunnen-doki da Saudiyya.