PDPn Arewa sun wancakalar da Shema, Ningi, sun zaɓi Iyorchia Ayu yayi takarar shugaban PDP

Shugaban shirya gangamin taron jam’iyyar PDP na Kasa wanda za a yi a ranakun 30 – 31 ga Oktoba, gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya ce gaba ɗaya ƴan Jam’iyyar sun na yankin Arewa sun zabi Iyorchia Ayu, tsohon shugaban majalisar dattawa wanda za su mara wa baya a zaben shugaban jam’iyyar.

Fintiri ya ce sanata Abdul Ningi da tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shema da kansu suka janye daga takarar.

Fintiri ya kara da cewa yanzu za su koma su tattauna da ƴan uwansu gwamnonin kudu domin kada a samu matsala a lokacin zaɓen.

A jawabin sa na amincewa da tsaida shi da gwamnonin kudu suka yi, Ayo ya ce lokaci yayi da PDP za ta dawo da martabarta a idanun ƴan Najeriya.

” ‘Yanzu gari ya waye wa ƴan Najeriya, ba a gaya wa makaho ana ruwan sama’. Ƴan Najeriya sun ɗanɗana APC kuma tabbas suna kewar PDP.

” Ina tabbatar muku cewa da zarar an kammala gangamin PDP da za ayi a ƙarshen wannan wata, za mu dawo mu fara aikin haɗa kan ƴaƴan jam’iyya. Za mu tattauna da kowa kuma zamu yi kokarin sasantawa da ɗinke barakar da ta kawo mana rarrabuwar kai.

Idan yayi nasarar zama shugaban jam’iyyar, zai zama mutum na uku kenan dan asalin jihar Benuwai da suka shugabanci jam’iyyar tun daga 1999.

Audu Ogbe da Gemade duk sun shugabanci jam’iyyar.