NSCDC ta kama lalataccen Uban dake kwana da ƴar cikin sa kamar matar sa

Rundunar Sibul Fefens NSCDC a jihar Ogun sun kama wani magidanci mai suna Rojaiye Balogun dake da shekaru 65 da laifin yi wa ‘yar sa mai shekara 17 fyade.

Shugaban rundunar Kolawole Taiwo wanda ya sanar da haka ranar Alhamis ya ce rundunar ta samu labarin wannan mummunar abu da Balogun yake yi ne daga wajen kawun yarinyar da ya shigar da kara a ofishinsu.

Taiwo ya ce ba tare da bata lokaci ba rundunar ta gaggauta ta kamo Balogun ranar Laraba a kauyen Imomo dake Ijebu-Ode.

Ya ce a ofishinsu Balogun ya ce yarinyar agolansa ce ba shine ainihin mahaifin ta ba.

Taiwo ya ce tsohon ya ce mahaifiyar yarinyar ta kawo yarinyar gidansa ne tun tana ƴar shekara 10 bayan sun yi aure.

“Tsohon wanda ya nuna ya yi nadamar abin da ya aikata ya ce sau daya ya taba yin lalata da yarinyar kuma ma dai khudubar shaidan ne ya bi.

Taiwo ya ce yarinyar ta ce Balogun ya dade yana lalata da ita kuma ma dai karya yake yi shine ainihin mahaifinta.

“Yarinyar ta ce rashin bashi hadin kai da ta yi duk da Naira 1,000 da ya yi alkawarin zai bata ya sa ya danne ta ta karfin tsiya a wannan rana yayi abinda ya ga dama.

“Ta ce tun tuni ta fadi wa mahaifiyar ta abin da ke faruwa da ita amma mahaifiyar ta ki yarda da ita.

Taiwo ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike sannan idan ta kammala za ta kai Balogun kotu a yanke masa hukunci.