Nnamdi Kanu Ne Mai Ceton: Ƴan Kabilar Igbo magoya bayan shugaban IPOB Kanu a Kotu

Dandazon ƴan ƙabilar Igbo magoya bayan Nnamdi Kanu da suka yi cincirindon a kotun Abuja ranar Alhamis sun rika waƙa suna kiɗa suna shewa cewa su fa shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ne mai ceton su a Najeriya.

Sun riƙa tika rawa suna suka ga gwamnatin Najeriya kan tsare shugaban gaban su da ta yi.

Shari’ar Nnamdi Kanu

Babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraren ƙarar da aka gurfanar da gogarman neman kafa ƙasar Biafra, kuma Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, zuwa ranar 10 Ga Nuwamba.

Nnamdi Kanu a yau ta ƙarƙashin lauyoyin sa ya na ƙalubalantar cancantar tuhumar cin amanar ƙasa da ake yi masa a kotun.

A sabon roƙon da ya yi, ya nemi kotun ta yi watsi da shari’ar mai ɗauke da tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa.

Babbar Mai Shari’a Binta Nyako ya ce a dawo ranar 10 Ga Nuwamba, bayan da ofishin Antoni Janar ya yi gyare-gyare ga caje-cajen da ake yi masa.

Daga nan ta bada umarnin cewa a bar mutum uku su riƙa ziyarar Kanu a kowace ranar Alhamis.

“Kuma shi Kanu ɗin ne da kan sa zai zaɓi waɗanda ya ke so su ziyarce shi.

Har yanzu dai Kanu ya na tsare a Hedikwatar SSS. Sai dai kuma roƙi kotu ta maida shi gidan kurkuku, amma kuma Mai Shari’a Binta Nyako ba ta amince ba.

Tun da farko dai SSS sun gabatar da Kanu a kotu, inda aka haye da shi a sama kan neme na biyar a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, misalin ƙarfe 9:45 na safe.

Sun isa ya na tsakiyar karta-kartan jami’an tsaro, kowane ɗauke da bindiga.

An hana ‘yan jarida da dama da lauyoyi da dama shiga harabar kotun.

A ranar Litinin ne Ofishin Antoni Janar ya gyara tuhume-tuhume da Gwamnatin Tarayya ke yi wa Kamu, daga biyar zuwa bakwai.

Daga cikin caje-cajen da ake yi masa har da cin amanar ƙasa, yi wa ƙasa zagon-ƙasa, maƙarƙashiya da kuma ayyukan ta’addanci.