NDLEA ta kama hodar ibilis da wasu haramtattun kwayoyi da aka shigo da su Najeriya daga Brazil da Canada

Hukumar NDLEA ta kama hodar ibilis da ganyen Skunk masu nauyin kilogiram 126.95 da aka shigo da su kasan daga kasashen waje.
Kakakin hukumar Femi Babafemi da ya sanar da haka ranar a Abuja ya ce an boye wannan haramtattun kwayoyi a cikin ganyen shayi da aka sarafa da sauyoyin itatuwa sannan aka Saka su a cikin gwanjon motoci da aka dauko daga kasashen Brazil da Canada.
Ya ce hukumar ta yi wannan kame a filin jiragen saman Akanu Ibiam dake jihar Enugu da tashar Tincan dake jihar Legas.
Ya ce hukumar ta kama wani Eze Ikenna mai shekara 42 a jirgin saman Ethiopian Airline wanda ya taso daga kasar Brazil ya biyo ta Addis Ababa sannan ya sauka a filin jiragin saman Enugu ranar 20 ga Janairu.
“Hukumar ta kama Ikenna da kilogram 16.2 na hodar ibilis da ya boye a cikin kwalin ganyen shayi guda biyu.
Babafemi ya ce a ranar 18 ga Janairu a tashar Tincan dake jihar Legas hukumar ta kama kwantena mai lamba TCLU 7799237 dauke da kilogram 110.75 na ganyen wiwi a ciki.
“Bincike ya nuna cewa an an shigo da wiwin daga Montreal kasar Canada.
“An gano wiwi a cikin wasu motoci biyu kirar Toyota Sienna da Honda Pilot SUV daga cikin guda hudu din da aka shigo da su daga Canada.
Shugaban hukumar Buba Marwa ya yaba kokarin da jami’an hukumar ke yi wajen kama wadannan muggan kwayoyi.
Marwa ya hori jami’an hukumar su ci gaba da kokari domin ganin an kawar da sha da safarar muggan kwayoyi a kasar.