NDLEA ta kama dan Najeriya da ya hadiye kullin hodar ibilis 92 a filin jirgin saman Abuja

Hukumar hana sha, safara da ta’ammali da muggan kwayoyi ta kasa, NDLEA ta kama Okolie Nwabueze mai shekara 53 a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da kullin hodar ibilis 92 da ya shigo da su daga kasar Brazil.
Rundunar ta gano hodar ibilis din a cikin Nwabueze inda ta killace shi sai da ya yi bahayan su.
Kakakin rundunar Femi Babafemi ya sanar da haka ranar Lahadi.
Babafemi ya ce sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna Nwabueze dan asalin kauyen Mmaku ne dake jihar Enugu.
“Rundunar ta kama Nwabueze mahaifin yara biyu ranar 2 ga Satumba bayan ya sauko daga jirgin Brazil-Doha-Abuja.
“Nwabueze ya bar Najeriya ya koma zama a Mozambique a shekarar 2004 inda daga nan ya koma zama a kasar Brazil da iyalensa a shekaran 2017.
“Daga nan ne ya shiga sana’ar safarar muggan kwayoyi inda ya shigo da kullin hodar ibilis 92 za a biya shi Dala 4,000 ladar shigo da kwayoyin Najeriya.
Bayan haka hukumar ta kama wani Aliyu Kwasare mai shekara 42 a filin jirgin saman Aminu Kano yayin da yake kokarin fitar da sabuwar kwaya mai suna ‘Akuskura’ zuwa kasar Saudiyya.
Babafemi ya ce rundunar ta kama Kwasare ranar 5 ga Satumba yayin da ake duba matafiyan da za su shiga jirgin Ethiopia zuwa Riyadh.
“Hukumar ta gano cewa Kwasare dan asalin karamar hukumar Kware ne, jihar Sokoto amma yana zaune a Goron Dutse jihar Kano.
Sannan kuma hukumar ta kama wani Aliyu Abubakar da yayi kokarin fita da ganyen wiwi da ya boye a cikin robar man shafawa ‘Caro White’.