Nasarar da Mali ta yi akan Tunisia na nan daram duk da ruɗanin da aka samu a wasan – AFCON

Mahukunta a AFCON sun ce ba za a sake buga wasan kwallon ƙafa da aka buga tsakanin Mali da Tunisia ba wanda aka samu ruɗani kadin a kammala wasan.

Tunisia ta nemi a sake wannan wasa bayan alkalin wasa ya hura tashi har sau biyu kafin lokaci ya cika.

AFCON ta ce ba za asake wasan ba domin daga baya an nemi ƴan wasan su fito a ƙarisa buga dakikokin da suka rage a kammala wasan ba su fito ba.

Sai dai kuma wakilin ƙasar Tunisia ya ce a lokacin da aka buklƙaci ƴan wasan su fito dukkan su sun riga sun shiga wanka ba za su iya yin komai akai ba.

” Tun da nike shekaru sama da 30 ana fafatawa da ni a harkar ƙwallon kafa a duniya, ban taɓa ganin irin haka ba, inda alƙalin wasa zai birkice ya dagula wasa yadda wannan alkalin wasa yayi a wannan rana.

Yadda alkalin wasa ya dagula wasan kwallon ƙafa tsakanin Tunisia da Mali

Alƙalin wasan da ya hura wasa tsakanin Mali da Tunisia ya birkice, kwakwalwar sa ta dagule, ya ruɗe, inda ya hura tashi ana minti 85. Bayan an ankarar da shi kuma sai aka koma a ka ci gaba da wasa, hakan bai gamsar da shi ba bayan minti 4 kuma ya sake hura tashe kowa ya tafi gida, an tashi wasa.

Bayan minti hudu kuma sai ya sake hura tashi wato saura minti 1 a gama wasan.

Wannan alkalin wasa dai ya birkice inda wasan ta kusa kwace masa komai ya dagule. Ya baiwa Tunisia bugun daga kai sai gola, amma duk da cewa ba hakan ya hura wa usur ba.

Haka kuma ya danna wa wani ɗan wasan Mali jan kati a laifin da ake ganin bai cancanci jan kati ba.

Kasar Tunisia sun harzuka inda suka rika kai ƙara wa alkalan bayan fage suna korafin an cuce su.

Masu sharhi sun ce akwai sake domin wannan alkalin wasa ya tuzarta wasan cin kofin Afrika ne da ake yi a Kamaru.

” Akwai yiwuwar ba za a sake saka shi ya hura wasa a wannan gasa ba. Saboda, bayan sau biyu yana hura a je a huta na mintina 5, sannan ga bata lokaci da aka yi na canje-canjen ƴan wasa da kuma na laifuka da aka hura har da na bugun daga kai sai gola sau biyu, duk bai sa ya kara lokaci ba sai dai ma ragewa da yayi.” In ji Okocha.