Nan ba da dadewa ba harkallar muggan kwayoyi a Najeriya zai zama tarihi – Buba Marwa

Shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Najeriya za ta kawo karshen matsalar safara da ta’ammali da muggan kwayoyi a kasar.

Marwa ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a birnin New York kasar Amurka.

Ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya za ta rage wannan matsala ne idan hukumar NDLEA ta ci gaba da samun goyon baya daga wajen gwamnatin tarayya, masu ruwa da tsaki da kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje.

Marwa ya ce ta’ammali da safarar muggan kwayoyi a kasar nan na kama da annobar cutar Korona inda a dalilin haka ya zama dole a mike tsaye wajen ganin an toshe duk kafar da ake amfani da su wajen shigowa da shan muggan kwayoyi a Najeriya.

Ya kara da cewa hukumar na shirin bude ofisoshi a kananan hukumomin kasar nan amma rashin isassun ma’aikata ya hana hakan faruwa.

“Amma yanzu mun samu izinin kara yawan ma’aikata daga gwamnatin tarayya sannan nan ba da dadewa ba za mu fara bude ofisoshin mu a kananan hukumomi.

“Zuwa yanzu hukumar NDLEA ta hada hannu da hukumar UNODC domin horas da ma’aikatan da aka dauka.

” Sannan gwamnati ta fito da hanyoyi daga wannan shekara 2021 zuwa 2025 da za su taimaka wajen kawo karshen harkallar muggan kwayoyi a kasar nan.

Marwa ya ce hukumar za ta bude ofisoshin ta a tashoshin motoci da jirgin ƙasa domin kama masu safara da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.