Nan ba da daɗewa ba majalisa zata saka hannu a Ƙudirin kafa rundunar ‘Peace Corp’ – Doguwa

Shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya Alhassan Doguwa ya ce nan ba da dadewa ba majalisar zata saka hannu a ƙudirin kafa rundunar ‘Peace Corp’.
Kakakin rundunar ‘Peace Corp’ Mrs Millicent Umoru-Osakwuaoguwa ta ce Doguwa ya fadi haka ne a taron karfafa gwiwar kwamandojin rundunar dake jihohin Kano, Katsina da Jigawa da aka yi a jihar Kano ranar Alhamis.
Dogouwa ya yi alkawarin ci gaba da mara wa rundunar baya sannan da saka matasa masu shekaru 18 zuwa 45 cikin rundunar.
“Kamata ya yi a rika jawo hankalin matasa wajen aiyukkan ci gaba domin suma su bada nasu gudunmawar.
“A yanzu a shirye muke mu jawo hankalin matasa cikin harkan inganta al’umma musamman a wannan lokaci da kasar ke fama da rashin tsaro.
Bayan haka sanata Mas’ud Doguwa ya yi kira ga rundunar ‘Peace Corp’ da su rika mai da hankali wajen aikin su.
Babban sakataren ma’aikatar wasanni, matasa da ci gaba na jihar Kano Sa’id Magami ya ce gwamnati za ta dauki nauyin saka matasa cikin rundunar ‘Peace Corp’ a jihar.
Shugaban rundunar farfesa Dickson Akoh ya ce rundunar ‘Peace Corp’ na cikin rundunonin da ya fi aiki da matasa a Nahiyar Afrika.
Akoh ya yi kira ga matasa da su zauna lafiya sannan su hada kansu domin inganta al’umma baki ɗaya.