Najeriya na buƙatar yi wa matsalar tsaro ‘wankin-babban-bargo’ -Gwamnatin Amurka

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka mai Kula da Al’amurran Siyasa, Victoria Nuland, ta ce akwai matuƙar buƙatar Najeriya ta ɗauki batun matsalar tsaron ƙasar, ɗaukar gabagaɗi ta yi masa wankin babban bargo.
Haka Victoria ta bayyana a ranar Alhamis, a ziyarar kwanaki biyu da ta kawo, inda ta ƙara bayyana matsalar tsaro a Najeriya cewa ta zama wani babban shaiɗancin da ‘yan ta’adda ke yi su na rugurguza yankunan karkara.
“Amma mu abin da mu ke ƙoƙarin yi shi ne mu haɗa ƙarfi da Najeriya ta ƙarfafa hare-haren ƙasa da na ana sama a lokaci ɗaya.
“Saboda haka ina ganin idan muka bai wa Najeriya goyon baya za ta iya yi wa harkar tsaron ƙasar nan wankin-babban-bargo.
Victoria ta ce abu na farko shi ne a fara yin ƙoƙarin kakkaɓe ‘yan ta’adda daga yankunan karkara ƙarƙaf. “Amma fa tilas sai gwamnati ta samar da isasshen tsaro, nagartattun ‘yan sanda da kuma tsarin tsaro na cikin al’umma su-ya-su, sai kuma kayan inganta rayuwar jama’a da nagartacciyar gwamnati. Idan ba haka aka yi ba kuwa, to duk wani shiri ba zai yi tasiri ba. Saboda ‘yan ta’addar sake dawo maku za su yi.”
“Sannan kuma mu na buƙatar mu ga an ɗauki ƙwaƙƙwara kuma tsauraran matakai tsakanin ƙasashen da ke maƙautaka da juna, saboda waɗannan ‘yan ta’adda su na zirga-zirga da gararamba kan iyakoki daga wannan ƙasa zuwa waccan. Don haka akwai buƙatar mu yi wannan aikin tare.”
Sakatariyar ta kuma jinjina wa Najeriya dangane da irin gagarimin aikin ta ta ke yi kan tsaro, ba a Najeriya kaɗai ba, har ma a ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS bakiɗaya.