Na kama matata ‘Turmi da Taɓarya’ da ɗan uwana suna lalata – Magidanci a Kotun Abuja

Wani magidanci mai suna Justine Onu dake zaune Abuja ya roki kotun Jikwoyi ta raba auren sa da mai ɗakinsa a bisa zargin karuwanci da ta ke yi.
Onu ya shaida wa Alƙalin kotun ya raba auren sa da matarsa saboda shahara da gogewa da tayi wajen karuwanci da barikanci.
” Ba rinka ji Alkali, saboda tsantsagwarar lalacewa da karuwanci da matata ke yi, har hawan jini sai da ya kama ni, kullum bani da lafiya.
Saboda haka Onuu ya roki kotu ta raba auren haka nan, ya gaji kowa ya kama gaban sa.
Matar Onu ta ƙaryata zargin da mijinta yanke yi a kanta a lokacin da alkali Labaran Gusau ya nemi ta amsa zargin da mijinta ya yi akan ta.
Kotu ta ɗage cigaba da sauraren Shari’ar zuwa 8 ga wannan watan.