Mutum 395 sun kamu da cutar Shan-inna samfurin ‘Poliovirus Type 2’ a Najeriya – NPHCDA.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa mutane 395 ne suka kamu da cutar Shan inna sumfurin ‘Poliovirus Type 2’ a jihohi 27 da Abuja.

Shu’aib ya fadi haka ne a wani takarda da manema labarai suka samu ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce sumfurin ‘Poliovirus Type 2’ ta barke a dalilin rashin mai da hankali wajen ganin an yi wa kowani yaro allurar rigakafin cutar Shan inna.

Shu’aib ya kara da cewa dakatar da kiyaye matakan da gwamnati ta dauka domin dakile yaduwar cutar saboda cutar korona na daga cikin dalilan da ya sa cutar ta dawo mana gadan-gadan a kasar nan.

Cutar Shan inna

Cutar Shan inna cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin rashin tsaftace muhalli.

Kwayoyin cutar na shiga jikin mutum ta hanyar cin abinci ko Shan ruwan da ba shi da tsafta.

Rashin yi wa ya allurar rigakafin cutar, rashin kammala yin allurar rigakafin cutar da rashin cin abincin dake inganta garkuwar jikin yara na cikin hanyoyin dake sa cutar na rikida da yaduwa a kasar nan.

Idan ba a manta ba kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta nuna damuwanta akan yadda ake zargin Najeriya da yada cutar Shan inna wa kasashen duniya sannan da yadda kasan ta ƙasa mai da hankali wajen yi wa yara allurar rigakafin cutar.

Idan ba a manta ba a shekaran 2020 kungiyar yaki da cutar shan inna (POLIO) ta Nahiyar Afrika (ARCC) ta bai wa Najeriya shaidar rabuwa da Shan inna bayan kasan ta yi tsawon shekaru uku ba tare da cutar ta bullo ba.

Sai dai a shakran 2021 Shu’aib ya sanar cewa Shan inna Wanda ake kamuwa da ita a dalilin yin allurar rigakafin cutar ta kama mutum 121 a jihohi 12 a kasar nan.

Ya ce tun a shekaran 2016 zuwa yanzu ba a sak samun bullowar da Shan inna sumfurin ‘Wild Polio’ ba.

Matakin da gwamnati ta dauka

Shu’aib ya ce gwamnati za ta hada hannu da kungiyoyin bada tallafi domin Samar da isassun maganin allurar rigakafin cutar.

Ya ce zuwa yanzu jihohin Najeriya da Abuja sun fara yin allurar rigakafin zango na farko sannan gwamnati ta fara shiri domin ganin an fara yin allurar rigakafin cutar zangon na biyu a cikin wannan shekara.

Shu’aib ya tabbatar cewa gwamnati za ta dauki tsauraran matakan da za su taimaka mata wajen dakile yaduwar cutar.

Ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su taimaka wajen bada ‘ya’yansu domin yin allurar rigakafin a duk lokacin da za a fara yin allurar rigakafin.