Mutum 36 sun kamu da cutar Monkey Pox a jihohi 14 a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 141 da ake zargin sun kamu da cutar Monkey pox a jihohi 13 a kasar nan.

A baya adadin yawan da ake zargin sun kamu da cutar sun kai mutum 110 a Najeriya.

Hukumar ta sanar da haka a shafinta a yanar gizo ranar Juma’a.

Zuwa yanzu cutar ta yaɗu zuwa kasashen da basu da tarihin an taɓa samun bullar cutar.

NCDC ta ce daga cikin mutum 141 din da ake zargin sun kamu da cutar sakamakon gwaji ya nuna cewa mutum 36 ne suka kamu da cutar a jihohi 14 da Abuja daga ranar 1 ga Janairu zuwa 12 ga Yuni 2022.

Jihohinsu hada da Legas-7, Adamawa- 5, Delta- 3, River -3, Cross River -2, Kano -2, Bayelsa -2, Edo -2, Imo -2, Filato-2, Nasarawa -1, Niger -1, Oyo -1, Ondo -1 da Abuja-2.

A shekaran 2022 mutum daya mai shekara 40 dake fama da wani cuta baya ga Monkey Pox ya mutu.

Daga watan Satumbar 2017 zuwa ranar 12 ga Yuni 2022 an samu mutum 653 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 33.

Daga cikin mutum 262 din da aka gano an samu tabbacin cewa kashi 40.1% sun kamu da cutar a jihohi 23.

Jihohin sun hada da Rivers -55, Bayelsa -45, Legas – 37, Delta -32, Cross River -16, Edo -12, Imo -10, Akwa Ibom -7, Oyo -7, Filato -5, Adamawa -5, Enugu -4, Abia -3, Nasarawa -3, Benue -2, Anambra -2, Ekiti -2, Kano -2, Niger -2, Ebonyi -1, Ogun -1, Ondo -1 da Abuja-8.

Mutum 9 sun mutu a dalilin kamuwa da cutara jihohi shida daga Satumba 2017 zuwa 12 ga Yuni 2022.

Jihohin sun hada da Legos- 3, Edo -2, Imo -1, Cross River -1, Abuja -1 da Rivers -1.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka dake kasar Amurka CDC ta fitar da wasu sharudda da za su taimaka wa mutane musamman ma’auratan wajen kare kansu daga kamuwa da cutar yayin da suke jima’i.

Hukumar ta ce Kaurace wa juna, mutum zai iya yi wa kansa wasa har sai ya samu gamsuwa da rufe bangaren jikin da kurarrajin cutar suka feso a jikin mutum kafin a sadu.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, kasala a jiki, kumburin gaɓaɓu, fesowar ƙuraje da sauran su.

Ana kuma iya kamuwa da cutar idan mutum ya yi jima’i da wanda ya ke ɗauke da cutar.

Daga ranar 13 zuwa 26 ga watan Mayu mutum 257 ne suka kamu da cutar a kasashe 23 dake karkashin kungiyar duniya WHO.

Kasar UK ta fi fama da yaduwar cutar inda mutum 106 suka kamu, Portugal – 49 da Canada – 26.

Dakile yaduwar cutar Monkey Pox

WHO ta ce za ta kara zage damtse wajen dakile yaduwar cutar a kasashen da cutar ta bullo.

Kungiyar ta Kuma ce ta tanadi maganin rigakafin cutar karambau domin yi wa mutane allurar rigakafin cutar a kasashen da cutar ta bullo.

Ta ce akwai kuma wani maganin rigakafin cutar karanbau da kasashen Canada da Amurka ke amfani da shi Mai suna Modified vaccinia Ankara Bavarian Nordic strain ko kuma MVA-BN wanda duk za a hada ana amfani da su domin dakile yaduwar cutar.