MUSULUNCI A KASAR INYAMIRA: Yadda ba a dauke mu mutane ba, wulakancin yau da ban da na gobe – Malam Okonkwo

Musulunci a kasar Inyamirai wato yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya na cin karo da matsalolin gaske, kamar yadda wasu daga cikin ‘yan asalin yankin wanda musulmai ne suka bayyana.

PREMIUM TIMES ta yi tattaki har kasar Inyamirai domin yin tozali da musulman yankin da kuma jin yadda suka fafatawa da ‘yan uwan su wadanda ba musulmai ba.

” Da zarar an gane kai musulmi ne a nan, to shikenan fa ka zama abin kyama. babu wanda zai so ka matso shi. Da farko dai ‘yan uwanka ne za su fara wancakalar da kai, su kore ka daga gida. Maganan samun aiki kuwa ba shi ma kwata-kwata a cikin lissafin su, ba za su baka ba.
Mu fa ba a dauke mu mutane ba a wannan yankin, cin fuska, muzgunawa da kyamata kawai ake mana.” In ji Suleiman Njoku

Suleiman Njokwu shine limamin masallacin juma’a na Jihar Imo.

” A wannan yankin daga anji kai musulmi ne sai a rika yi maka kallon kai dan Boko Haram ne ko kuma wani dan ta’adda.

Shi kuma Mr Ugwu cewa yayi a dalilin kyamar su da ake yi a yankin kashi 90 cikin 100 na musulman dake yankin kudu masa Gabas, duk sun yi kaura zuwa Arewa domin a can ne za su iya yin addinin su ba tare da an muzguna musu ba.

” Haka kuma ‘yan kabilar mu, Igbo, basu kaunar ace wai kai Inyamiri ne amma kuma kana musulunci. Da zarar sun gane kana musulunci sai komai ya canja. Duk zumunta da soyayyar dake tsakanin ku sai ya lalace saboda kawai kace kai musulmi ne.

Musulman sun koka cewa da zarar wani abu ya da ka da wadanda ba musulmai ba sai su rika bi wuraren da kuke sallah suna konawa. ” Akwai wani rikici da aka yi tsakanin wata mata musulma da dan acab, amma abu kamar wasa har masallacin mu an kona shi. Gwamnan jihar mutum ne mai kirki, ya sa ake gina masallacin wanda ya fi na da kyau.

Shi ko Okonkwo cewa yayi idan har kaga makaranta ko masallaci da ake taruwa kullum ana sallah da sauransu, to wannan masallaci yana filin gwamnatin tarayya ne ko kuma unguwannin Hausawa.