MURNA TA KOMA CIKI: Kotu a Jalingo ta kori Bwala daga takarar gwamna na jam’iyyar APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo ta kori ɗan takarar gwamnan jihar Taraba na jami’iyyar APC Emmanuel Bwacha daga takara a zaɓen 2023.
Sanata Emmanuel Bwacha ne ke wakiltar Taraba ta Kudu a majalisar Dattawa kuma shine ɗan takarar gwamnan jihar Taraba a jam’iyyar APC.
Mai shari’ah Simon Amobeda wanda shine alkalin kotu kuma wanda ya yanke hukuncin ya umarci APC ta gudanar da wani sabon zaben fidda gwani cikin kwana 14 domin musanya Bwacha da kotu ta kora.
Daga nan sai Alkalin ya umarci hukumar zaɓe INEC da shi kan sa sanata Bwacha su daina ganin shi Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a jihar.
Idan ba a manta ba David Sabo Kente, daya daga cikin masu neman takarar gwamna a APC ya shigar da karar kalubalantar zaɓen fidda gwani wanda jam’iyyar ta yi a jihar Taraba. Kente ya ya ce jam’iyyar bata yi zaɓe ba ɗauki ɗori ta yi.
Sannan kuma baturen zaɓe ya bayyana sakamakon karya bayan da aka yi zaɓen.
Sai dai kuma akwai yiwuwar masu kare Bwacha su ɗaukaka kara.