MUMMUNAN HATSARIN KANO: Kwale-kwale ya kife da ɗalibai da fasinjoji sama da 50 a Kogin Ɓagwai, an ceto 7 da ran su, ana neman sauran

Wani kwale-kwale ɗauke da yara ɗaliban Islamiyya da aka ce sun fi 50, ya kife a cikin Kogin Ɓagwai a ranar Talata.

Ɗaliban waɗanda ‘yan makarantar Islamiyya ne daga garin Badau, su na kan hanyar su ne zuwa Ɓagwai, hedikwatar ƙaramar hukumar, inda daga can kuma za su zarce taron Maulidi a garin Tofa.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Koyawa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an samu ceto mutum bakwai daga cikin su. Amma kuma ana ci gaba da nemo sauran.

Wata majiya ta shaida wa Premium Times cewa akasarin waɗanda aka rasa inda su ke ɗin sun mutu.

Sannan kuma wani mai suna Abubakar Arɗo, ya shaida wa wakilin mu cewa an lafta wa kwale-kwalen mutane sama da 50, waɗanda sun fi ƙarfin yawan mutane da ya kamata ya ɗauka a lokaci guda.

Ya ce har yanzu dai ana ta laluben neman sauran ɗaliban da sauran fasinjojin.

Idan ba a manta ta a wannan ruwa ne cikin 2008 jirgin ruwa ya kife da tawagar ‘yan kai amarya, har mutum 26 su ka mutu.