MUGUN JI DA MUGUN GANI: Mai dadiro ya kashe kwarto a ɗakin farkar su

‘Yan sanda sun kama wani mutum da ke zaman dadiro da wata mata, bayan ya kashe wani da ya samu kwance tare da ita, a cikin ɗakin ta.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun sun tabbatar da kama wani mutum mai suna Bisi Omoniyi, bayan ya kashe Akinyemi Alani a ɗakin farkar sa mai suna Kafayat Sakariyau.

Mummunan lamarin ya faru a garin Ajilete da Jihar Ogun a ranar 15 Ga Oktoba, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya sanar wa manema labarai a garin Offa.

Ya ce afkuwar kisan ke da wuya sai aka sanar da DPO Olabisi Elebute na Dibijin ɗin Owode Egbodo a garin Ajilete.

“Yayin da DPO ya tura jami’an tsaro, sun iske gawar Akinyemi Alani a cikin ɗakin Kafayat, su ka su ka iske wanda ake zargi da kashe shi ɗin, Bisi Omoniyi. Sai dai matar, wato Kafayat, ta gudu ba san inda ta ke ba.” Inji PPRO Oyeyemi.

“Wanda ake zargi ya aikata kisan ne a lokacin da ya je ɗakin Kafayat da niyyar kwana tare da ita a cikin ɗakin. Sai dai kuma ya samu ɗakin an kulle ta ciki, saboda ta na tare da wani farka wanda ya riga shi zuwa.

“Ya yi ta buga ƙofar, amma su ka ƙi budewa. Daga baya ya yi kukan-kura ya ɓalle ƙofar, inda ya same su kwance tare a kan gado.

“Bisi Omoniyi ya rarumi wata adda wadda ke ajiye a cikin ɗakin, ya riƙa kafta wa Akinyemi Alani sara, har ya kashe shi.”

Kakakin Yaɗa Labarai ya ce ‘yan sanda sun garzaya da shi asibiti, amma su na isa likitan da ya duba shi, ya ce ya mutu.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole ya umarci a maida wanda ya yi kisan da Sashen Binciken Masu Manyan Laifuka a ci gaba da tsare shi, kafin a gurfanar da shi kotu, bayan an kammala bincike.