MONKEY POX: Mutum 524 sun kamu, mutum 12 sun mutu a Afirka

Sakamakon yaduwar cutar monkey pox da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar ya nuna Najeriya ce a gaba a kasashen da cutar ke yaduwa da kisar mutane a Afrika.

Shugaban kungiyar reshen Afrika Matshidiso Moeti ce ta bayyana haka a taron da ta yi da manema labarai inda ta yi karin bayani akan yaduwar cutar bakon dauro a Nahiyar Afrika.

Moeti ta ce alkaluman yaduwar cutar monkey pox da aka fitar ranar 8 ga Satumba 2022 ya nuna cewa mutum 524 sun kamu kuma cutar ta yi ajalin mutum 12 a kasashen Afrika 11.

Ta ce Najeriya ita ce kasar da ta fi fama da yaduwar cutar, sai kuma Jamhuriyyar Kongo da kasar Ghana.

Moeti ta ce cutar ta yi ajalin mutum shida a Najeriya daga cikin mutum 12 din da suka mutu a Afrika inda kasar Ghana na da hudu sannan Jamhuruyyar kasar Kongo na da biyu.

Sakamakon yaduwar cutar da hukumar CDC ta tattaro na ranar 9 ga Satumba ya nuna cewa mutum 220 ne suka kamu da cutar a Najeriya, Jamhuruyyar Kongo mutum 195 sai kasar Ghana mutum 76.

Zuwa yanzu mutum 57,527 ne suka kamu da cutar a duniya.

Ko da yake Nahiyar Afrika bata samu maganin allurar rigakafin cutar ba amma WHO ta bata gudunmawar kayan yin gwajin cutar domin inganta yi wa mutane gwajin cutar a Nahiyar.

Bakon dauro a Afrika

Da take bayanin nasarorin da Afrika ta samu wajen dakile yaduwar cutar bakon dauro Moeti ta ce Afrika ta cika shekaru biyar ba ta samu bullarvbakon dauro nau’in A a nahiyar ba.

Sai dai ta ce bullowar cutar korona ta dakatar da yi wa yara sama da miliyan 50 allurar rigakafin cutar a Afrika.

Moeti ta ce alamun bakon dauro nau’in rukuni C ta barke a kasashe 7 dake Kudu da Saharan Afrika a cikin shekara 9.

Ta ce a shekarar bara cutar ta yi ajalin mutum sama da 200 a Jamhuriyyar Kongo.