MONKEY POX: Mutum 21 sun kamu a cikin mako daya a Najeriya – NCDC

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 21 sun kamuwa da cutar monkey pox a Najeriya cikin kwanaki 7 da suka gabata.

NCDC ta ce cutar ta yi ajalin mutum shida a jihohi shida dake kasar nan daga watan Janairu zuwa Agustan 2022.

Wadannan jihohi sun hada da Delta, Lagos, Ondo, Akwa Ibom, Taraba da Kogi.

Yaduwar cutar

NCDC ta ce adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya karuwa zuwa mutum 241 a cikin sati daya daga ranar 15 zuwa 21 ga Agusta bayan da mutum 21 suka Kara kamuwa da cutar a kasan.

Hukumar ta ce an gano mutum 21 din da suka kamu da cutar a jihohi 12 da suka hada da Lagos –7, Adamawa – 2, Ebonyi – 2, Imo -two, Akwa Ibom – 1, Anambra –1, Edo – 1, FCT – 1, Katsina State – 1, Kaduna State – 1, Kogi –1 da Ondo State – 1.

NCDC ta ce jihar Legas ce jihar da ta fi fama da yaduwar cutar inda a jihar mutum 42 ne suka kamu da cutar.

Tun bayan bullowar cutar a Satumba 2017 zuwa Agusta 2022 an gwada mutum 1,116 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 35 inda daga ciki mutum 467 sun kamu a jihohi 32 da Abuja.

Cutar ta yi ajalin mutum 14 a jihohi 10 da suka hada da Lagos –3, Edo – 2, Imo –1, Cross River – 1, FCT – 1, Rivers – 1, Ondo State –1, Delta – 1, Akwa Ibom – 1, Taraba – 1 da Kogi – 1.

Cutar Monkey pox

Cutar ‘Monkey Pox’ cuta ce da take kama fatar mutum inda zaka ga mai dauke da cutar na fama da wasu irin manya-manyan kuraje kamar kazuwa.

Cutar ya fara bullowa a Nahiyar Afrika a shekarar 1970 sannan ya bayyana a shekaran 1978 a Najeriya.

Tun daga wancan lokaci cutar bata sake bayyana ba sai a shekarar 2017 a jihar Bayelsa.

Hanyar da cutar Monkey pox ke shiga jikin mutum

Rahotanni sun nuna cewa namun daji kamar su birai da beraye dake shawagi a gidajen mutane na daga cikin ababen dake kawo cutar ‘Monkey Pox’.

Sannan kuma cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.

Ana kuma iya kamuwa da cutar idan aka yi jima’i da wanda ya ke ɗauke da cutar.

Alamun cutar sun hada da Zazzabi, yawan jin gajiya a jiki, ciwon jiki musamman baya, kumburin jiki musamman idan cutar ta fara nunawa, bayyanan kuraje a jiki.

Hanyoyin da za a bi domin guje wa kamuwa da cutar.

1. A daina cin naman dabbobin daji kamar su biri, burgu da bera.

2. A hana dabbobi yawo musamman wadanda ke kiwon su domin kada su fita su dauko cutar daga jikin dabbobin da suke dauke da cutar kuma a killace dabbobin da suka kamu da cutar saboda hana yaduwar ta.

3. Mutane su nisanta kansu daga dabbobi musamman daga kashin su da kuma jikinsu.

4. Kada a zauna daki daya da mutanen da suka kamu da cutar.

5. A yi amfani da safan hannu wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar musamman ma’aikatan asibiti sannan idan aka ziyarci wanda ke dauke da cutar a tabbatar an wanke hannaye da ruwa da sabulu bayan an fito.

6. A tabbatar cewa a kowani lokaci ana tsaftace muhalli.

7. Sumbatar mai dauke da cutar kan iya sa a kamu.

8. A rage shan hannu ko ta yaya sannan a yi amfani da man tsaftace hannu.

9. Hukumar dakile yaduwar cututtuka dake kasar Amurka CDC ta ce Kaurace wa juna, mutum zai iya yi wa kansa wasa har sai ya samu gamsuwa da rufe bangaren jikin da kurarrajin cutar suka feso kafin a sadu.