Me ya sa Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa ke maimaita sutura? Daga Maishanu Ahmadu

Wani bincike da aka yi ya nuna yadda mai martaba Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ke yawan maimaita sutura wanda hakan ya zama bambarakwai a al’adar Sarakuna masu daraja ta ɗaya.

An bi shafin masarautar Rano da ke dandalin Instagram inda aka ga wasu daga cikin hotunan da Sarkin ya maimaita kayan da ya saka a mabambantan lokuta. Misali kayan da ya saka ranar 2 ga watan Yuli lokacin da ya karɓi shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA, Malam Kashifu Inuwa su ya maimaita su a ranar 17 ga watan Satumba.

Wani misalin kuma kayan da ya saka a ranar 4 ga watan Satumba su ya sake maimaita wa ranar da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a ranar 5 ga watan dai na Satumba a fadar sa da ke birnin tarayya Abuja. Haka kuma suturar da ya saka a ranar 27 ga watan Satumba ita ya maimaita ranar 28 ga watan Satumba, inda ya halarci fadar gwamnatin Kano domin shaida baiwa sabon Sarkin Gaya takardar kama aiki da Ganduje ya yi.

Wani ƙarin misali kuma shi ne kayan da ya saka a lokacin zaman fada na ranar 11 ga watan Oktoba su ya maimaita ranar 15 ga watan a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin Abdulkarim Abdulsalam Zaura a fadarsa.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Mayun shekarar 2020 ne Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya naɗa Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa a matsayin sabon sarkin Rano. Kafin nadinsa, Alhaji Kabiru ya kasance hakimin Kibiya kuma Kaigaman Rano.

Hakazalika Sarkin Rano na ɗaya daga cikin sarakuna huɗu masu daraja ta ɗaya na sababbin masarautun jihar Kano da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira.

Bugu da ƙari kuma da aka yi la’akari da yadda Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kere Sarkin na Rano musamman harkokin da su ka shafi sutura da abin hawa duk da cewa dukkanin su sarakuna ne masu daraja ta ɗaya.

Domin abu ne mai wahala ka ga Sarkin Kano ya maimaita sutura kuma ya kan yi amfani da motocin alfarma irin su Rolls Royce da Limousine da kuma sauran motoci na kece raini a duk lokacin da zai fita zuwa wani guri.

Amma shi Sarkin na Rano har kawo yanzu yana amfani da motocin da gwamnatin Kano ta siya musu tare da sauran Sarakunan guda huɗu.

A bisa al’adar Sarakuna masu daraja ta ɗaya a arewacin Najeriya ba kasaifa akan ga Sarki ya kan maimaita sutura a kwana kusa ba kuma ya kan yi ƙoƙarin kece raini a tsakanin ƴan uwansa sarakuna.