Matsin Tattalin Arziki Ke Sa Matasa Tserewa Zuwa Kasashen Duniya – Moghalu

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN kuma dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, Kingsley Moghalu, ya alakanta yawan barin kasar da matasa ke yi a halin yanzu ga matsin tattalin arziki da rashin kyawun yanayin rayuwa.